Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Massnoor Tech Hub Ta Gudanar da Horon Rana Ɗaya Kan Ayyukan Kwamfuta da yadda ake shiga Intanet Ga Matasa

Daga Ibrahim Muhammad  A ƙoƙarinta na ci gaba da bai wa matasa damar samun ilimin zamani, MASSNOOR TECH HUB ta shirya wani horo na musamman ...


Daga Ibrahim Muhammad 

A ƙoƙarinta na ci gaba da bai wa matasa damar samun ilimin zamani, MASSNOOR TECH HUB ta shirya wani horo na musamman na yini guda kan Ayyukan Kwamfuta da yadda ake shiga Intanet ga matasa. An gudanar da wannan horo ne a ofishin Massnoor Tech Hub da ke Sabon Gari, Zariya, Jihar Kaduna.

Wannan horo ya haɗa matasa masu shekaru tsakanin 6 zuwa 15, daga makarantu daban-daban na gwamnati da masu zaman kansu da ke Zariya, ciki har da Zenith Academy, GSS Dogon Bauchi, Great Golden Height, GSS Chindit Barracks, ADUMAS Model College, da Prestige Leadership Academy.

Babban jami’in Gudanarwa (COO) na Massnoor Tech Hub, Ammar Muhammad Rajab, ya bayyana cewa manufar horon ita ce gabatar da ɗalibai ga fahimtar asalin amfani da kwamfuta, sanin sassa na kwamfuta, yadda ake sarrafa tsarin kwamfuta, da kuma amfani da intanet cikin tsaro. 

Ya ce: “Muna da yaƙinin cewa ya kamata a tare su tun suna ƙanana. Wannan shiri an tsara shi ne don kafa tubalin ilimin ICT ga ɗalibai da kuma nuna musu yadda za su yi amfani da intanet ta hanya mai fa’ida.”

Horarwar ta ƙunshi ayyukan a aikace, inda ɗalibai suka koyi yadda ake kunnawa da kashe kwamfuta, amfani da manhajojin rubutu kamar word processor, yadda ake rubuta takardu, buga su, da kuma kewayawa a intanet don nemo bayanai masu amfani da suka shafi karatu.

A ƙarshen horon, dukkan mahalarta sun samu Takardar Kammala Horo (Certificate of Completion) a matsayin shaida ta sabbin ƙwarewar da suka samu.

Ɗaya daga cikin mahalarta, Zainab Muhammad, ta bayyana farin cikinta da cewa:b “Kafin wannan horo, ban san komai game da kwamfuta ba. Amma yanzu na iya kunnawa da kashe kwamfuta, rubuta takarda, har ma da buga ta.”

Wani ɗalibi kuma, Abdulhakim Saidu, ya ce cikin alfahari: “Yanzu zan iya amfani da kwamfuta da kuma kewayawa a intanet don neman muhimman bayanai. Ina matuƙar godiya da wannan dama.”

Ɗaliban sun nuna jin daɗinsu bisa horon, inda da dama daga cikinsu suka ce suna fatan samun damar halartar irin wannan horo a nan gaba.

Wannan shiri na Massnoor Tech Hub wani babban mataki ne na rage gibin fasahar zamani a tsakanin al’umma da kuma samar da muhimman ƙwarewar ƙarni na 21 ga matasa.

No comments