Daga Awwal Umar Kontagora Shugaba Bola Ahmed Tinubu, GCFR, ya amince da sabunta nadin Alhaji Abubakar Sadiq Yelwa a matsayin Man...
Daga Awwal Umar Kontagora
Shugaba Bola Ahmed Tinubu, GCFR, ya amince da sabunta nadin Alhaji Abubakar Sadiq Yelwa a matsayin Manajan Darakta kuma Babban Jami'in Gudanarwa na Hukumar Raya Yankunan da ke Samar da Wutar Lantarki ta Ruwa ta Kasa (N-HYPPADEC) don wa'adi na biyu kuma na karshe na shekaru hudu (4).
A cikin wata sanarwa da Segun Imohiosen, Daraktan Yada labarai da hulɗa da jama'a na ofishin Sakataren gwamnatin Tarayya ya fitar, ya ce nadin nasa bisa tanadin Sashe na 93 na dokar wutar Lllantarki ta 2023.
Shugaban ya bukace shi da ya karfafa kan nasarorin da hukumar ta samu tare da kawo sabbin abubuwa da himma wajen sauke nauyin da aka dora masa.
No comments