Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

An nemi ƙungiyoyin Fulani da su tashi tsaye wajen wayar da kan makiyaya muhimmancin mallakar katin zaɓe

Daga Awwal Umar Kontagora An nemi kungiyoyin Fulani da su tashi tsaye wajen wayar da kan makiyaya muhimmancin mallakar katin zab...

Daga Awwal Umar Kontagora

An nemi kungiyoyin Fulani da su tashi tsaye wajen wayar da kan makiyaya muhimmancin mallakar katin zabe, domin da katin zabe ne kawai za mu iya mayar da bukin da gwamnatin tai wa makiyayan jihar nan. Daraktan Fulani Youth Sai Bago Again, Alhaji Shehu Umar Jita ne yayi kiran lokacin da yake zantawa da manema labarai.

Alhaji Shehu Umar, ya cigaba da cewar kudurin gwamnatin Umaru Bago shi ne tabbatar da al'ummar Fulani da Makiyaya sun samu zaman lafiya, wanda sanin kowa ne a kokarin ma'aikatar kula da jin dadin makiyaya da manoma, bisa jagorancin Hon. Umar Ahmed Sanda an samu sulhu a bangarori da dama, wanda hakan na daga kudurin babban manomin jiha, Dakta Umaru Bago, saboda haka wajibi ne mu fito dan marawa wannan gwamnatin.

Daraktan, ya cigaba da cewar manyan kungiyoyin Fulani da su tashi tsaye wajen shiga lungu da sako da ba a kafafen yada labarai kadai ba wajen ganin mun mallaki katin zabe musamman ga matasan mu masu tasowa, dan ganin mun baiwa marada kunya a lokacin zaben nan na tafe.

Da ya juya kan zagon kasa da ake yiwa sabuwar ma'aikatar jin dadin makiyaya, ya shawarci mai girma kwamishina da ya kara bude idonsa sosai, akwai ma'aikatan da yake tufka suna walwale ma shi, wanda burin mu shi ne wanzuwar ma'aikatan ta yadda yaya da jikoki zasu ci moriyar wannan ginshikin mai albarka da Bago ya assasa.

Yace mu a tafiyar mu duk wani mai son cigaban jihar Neja ta hanyar bunkasar tattalin arziki, zaman lafiya muna tare da shi. Fulani makiyaya da Manoma ba yan ta'adda ba ne, muna goyon bayan gwamnati da jami'an tsaro wajen daukar duk matakin da za a dauka na ganin an tsalkake al'umma daga tsoro ko fargabar duk wani abinda zai kawo masu cikas wajen gudanar da rayuwarsu ta yau da kullun.
Ya zama wijibi shugabannin Fulani da sarakuna da su hada kai wajen sanya idanu da nusar da gwamnati duk wani barazanar tsaro, sannan su tabbatar sun yaki rashawa ta hanyar tona asirin duk wani shugaba da aka samu da hannu wajen belin yan ta'adda, domin gatar da ake nunawa masu laifi ta hanyar karban belinsu ne ya assasa matsalolin da suke kokarin gagarar kundila a halin yanzu kuma wannan tamkar yiwa kokarin gwamnati ne na inganta rayuwar al'umma da zaman lafiya zagon kasa.

No comments