Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Mu A Rijau Babu Sauran Adawa Da Gwamnatin Bago - Hamdala

Daga Awwal Umar Kontagora An nemi al'ummar Rijau da su cigaba da goyawa gwamnatin Manomi Umaru Mohammed Bago baya, saboda sa...

Daga Awwal Umar Kontagora

An nemi al'ummar Rijau da su cigaba da goyawa gwamnatin Manomi Umaru Mohammed Bago baya, saboda samun nasarar ayyukan da ya sanya a gaba. Wani tsohon dan siyasa kuma jigo a jam'iyyar APC mai mulki, Alhaji Muhammad Lawal Ibrahim ( Hamdala) yayi kiran lokacin da yake tsokaci kan ayyukan raya kasa da gwamnatin Bago ta sanya a gaba.

Hamdala ya cigaba da cewar mun fi karfin shekaru hamsin muna fafutuka tun da karfin mu gaya yau rashin lafiya ya tsugunar da mu amma ran mu gwamnatin nan ta saurari koken mutanen Rijau kan hanyar Kontagora zuwa Rijau da ta hade mu da jihar Kebbi an fara ta kuma aiki na tafiya babu kama hannun yaro, abinda muke fata shi ne Allah ya karfafi gwuiwar gwamna Bago ya kammala aikin nan da hannunsa na alheri da ya somo.

Babban abinda ke ci mana tuwo a kwarya yasa da yawan mu masu fama da lalura muka kasa ziyartar yan uwa, shi rashin hanya da matsalar tsaron da ya daidaita al'ummomin mu.

Muna fatar yadda aka somo aikin hanyar nan, matsalar tsaro ya zama tarihi a kasar Rijau, ba mu adawa da gwamnatin nan, kuma a shirye muke mu karfafa guiwar al'ummar mu wajen sake bada kuri'unsu ga gwamna Umaru Mohammed Bago fiye da wanda suka bayar a zaben gwamna da ya gabata.

Kammala aikin hanyar nan zai farfado da tattalin arzikin kasar Rijau, karkarun da suka watse saboda damuwa, da yardar Allah zasu dawo da martabar su fiye da baya, noma, kasuwanci da kiwo da aka san kasar Rijau da shi zai inganta.

Dattijon ya shawarci yan adawa da masu sukar gwamnatin nan da su mayar da wukarsu kube domin talaka yasan gwamnatin nan mai sauraren koken jama'a, domin ayyukan da ta sanya a gaba zahiri ne ba kumbiya kumbiya ba. Kamar yadda gwamna Bago ya lashe zabe a zaben da ya gaba zai sake lashe wannan zaben da gagarumin rinjaye, inji shi.

No comments