Daga Hussaini Yero Jam’iyyar PDP reshen jihar Zamfara ta koka kan yadda sojojin Najeriya suka goyi bayan 'yan Jamiyyar APC ...
Daga Hussaini Yero
Jam’iyyar PDP reshen jihar Zamfara ta koka kan yadda sojojin Najeriya suka goyi bayan 'yan Jamiyyar APC wajan tarwatsa 'yan Jamiyyar PDP a Runfunan zaben cike gurbi da aka kammala na Kaura Namoda ta Kudu wanda hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar INEC ta bayyana cewa bai kammala ba.
Shugaban jam’iyyar PDP na jihar, Hon Jibo Magayaki ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai kan matsayin jam’iyyar a zaben cike gurbi na mazabar Kaura Namoda ta Kudu a Hedikwatar ofishinsa da ke Gusau babban birnin jihar.
Shugaban na jihar ya kara da cewa, “Mun kira ‘yan jaridu ne a yau domin nuna matukar damuwa kan abin kunya da ya faru a zaben cike gurbi na ranar 16 ga watan Agusta a mazabar Kaura Namoda ta Kudu.
"Abin da ya kamata zabe ya zamo na lumana dan bunkasa dimokuradiyya, abin takaici ne ya rikide zuwa tsoratarwa, tashe-tashen hankula da magudin zabe wanda jam’iyyar adawa ta APC ta jihar ta shirya tare da Sojojin Najeriya.
“Maimakon samar da isasshen tsaro, da yanayin aiki cikin lumana, jami’an soji dauke da muggan makamai sun kasance a runfunan zabe, ba wai don samar da tsaro ga masu zabe ba sai dai don muzgunawa, tsoratarwa ga fararen hula masu kada kuri’a.
“An yi wa 'yan jami’an PDP duka a unguwannin duka, an kore su, an hana su shiga rumfunan zabe .
“A Unguwar Sakajiki babu zabe kwata-kwata, an sace akwatunan zabe, takardu da sauran muhimman abubuwa, sannan aka kirkiri sakamakon da jam’iyyar APC tare da sauran ‘yan uwansu suka kirkiri ba tare da wakilan jam’iyyar PDP ba a dukkan shiyya shida da suka halarci zaben.
“A cewarsa , dokar zabe da ka’idojin INEC sun nuna cewa dole ne jami’an soji su kiyaye akalla tazarar mita 50 daga rumfunan zabe, amma a fili karara da saba doka, an ga sojoji a tsaye kai tsaye a cikin rumfunan zabe suna raka akwatunan zabe tare da taimakawa wajen magudin zabe.
“An turo manyan jiga-jigan gwamnatin tarayya,da Sojoji ba wai a kan ‘yan "Yan bindiga da masu aikata laifuka ba, a’a, a kan masu jefa kuri’a marasa laifi da kuma adawa da dimokuradiyyar jihar Zamfara.
“Abin da ya fi tayar da hankali shi ne bayanan sirri da aka samu cewa an yi amfani da wasu ‘yan bindiga wajen tursasa masu kada kuri’a a wasu sassan mazabar Kaura Namoda ta Kudu suna cewa “idan wani mai zabe ya kada kuri’a ga PDP, ba zai dawo gida da rai ba.
“Wannan dabi’ar dabbanci da rashin son zuciya,ya sabuwar doka ce da aka yi ta a karkashin jam’iyyar APC, kuma ba za ta samu karbuwa a wajen al’ummarmu ba.
“Jam’iyyar PDP ta yi kakkausar suka tare da nuna rashin amincewa da wannan magudi da jam’iyyar APC ta yi ba bisa ka’ida ba da kuma rashin da’a.
“Duk da yanayin tsoro da fargaba, jam’iyyar PDP ta jihar Zamfara tana alfahari da jajircewa da magoya bayanta da mutanen Kaura Namoda ta Kudu suka nuna a matsayinsu na jam’iyyar PDP da Gwamna Dauda Lawal.
“Muna kira ga duk masu biyayya da magoya bayan jam’iyyar PDP da su kwantar da hankalinsu tare da bin doka da oda yayin da muke amfani da duk wata hanya ta doka da ta tsarin mulki don kalubalantar da fallasa wannan zaben da aka yi wa jama’a.
No comments