Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

JFCIN ta zabi Ambassada Dr. Nura Hashim mataimakin shugaban kungiyar ta kasa

Daga Awwal Umar Kontagora Ƙungiyar hadin guiwa ta "Farmers Community Initiative of Nigeria" (JFCIN) ta sanar ta zabi Amb. (Dr) Nur...


Daga Awwal Umar Kontagora

Ƙungiyar hadin guiwa ta "Farmers Community Initiative of Nigeria" (JFCIN) ta sanar ta zabi Amb. (Dr) Nura Hashimu (Tallafin Bosso Karami) matsayin Mataimakin Shugaban Ƙungiyar ta Ƙasa.

An tabbatar da wannan nadin ne a hukumance a yayin bikin ƙaddamar da fara shuka ta ƙasa da kuma kaddamar da taraktoci da aka gudanar a yau Laraba a garin Oyo ta Jihar Oyo.

A wata takardar manema labarai da ya samu sa hannun Comrade Alhaji Aliyu Abdullahi Mai Magana da Yawun kungiyar na Ƙasa (National PRO), JFCIN. Yace an miƙa takardar nadin ne a madadin babban jagoran Ƙungiyar (Grand Patron), Mai martaba sarkin Oyo, Iku Baba Yeye, Oba Abdulakeem Abimbola (Owoade I), Alaafin na Oyo Land. Sai dai Mai martaba Alaafin ya samu wakilcin Mai martaba, Alhaji Dr. Ahmadu Haruna Maiyasin II, CON, JP, GFNY, Sarkin Sasa, Sardaunan Yamma kuma Shugaban Majalisar Sarakunan gargajiya na Arewa a jihohi sha bakwai na kudancin Nijeriya.

A cikin jawabin sa, Shugaban na Ƙasa na JFCIN, Comrade Adekunle Adebayo, ya bayyana shirin noma na musamman da ƙungiyar ta tsara, wanda ya haɗa da:

1. Noman hektar 100 na ridi a jihar Neja a wannan damina ta bana na shekarar 2025.

2. Noman hektar 5,000 na masara, shinkafa, waken soya da auduga a daminan shekara mai zuwa ta 2026.

3. Raba taraktoci guda 100 ga ƙungiyoyin manoma a matsayin rance.

4. Faɗaɗa Agric Microfinance Bank na ƙungiyar zuwa jihohin Neja, Delta, Gombe da Kano nan da shekarar mai zuwa ta 2026 domin ƙara tallafa wa manoma.

Ƙungiyar ta tabbatar da nadin Malam Sani Muhammad Danladi a matsayin shugaban ƙungiyar a jihar Neja.

Ƙungiyar ta jaddada aniyar ta na ci gaba da tallafa wa manoman Nijeriya ta hanyar amfani da injina na zamani, bayar da tallafin kuÉ—i da kuma noman manyan filaye. Haka kuma, ta bayyana cewa sabon Mataimakin shugaban Ƙasa, Amb. Dr. Nura Hashimu, zai taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da cimma waÉ—annan manufofi. 


No comments