Daga Muhammad Farouk Ciroman Zazzau Saidu Mailafiya da Sarkin Zazzau Ahmed Nuhu Bamalli, ya cire wa rawaninsa bisa zarginsa ...
Ciroman Zazzau Saidu Mailafiya da Sarkin
Zazzau Ahmed Nuhu Bamalli, ya cire wa rawaninsa bisa zarginsa da cewa ba ya yi
wa Sarkin biyayya, ya bayyana Sarkin Zazzau, Ahmed Nuhu Bamalli da cewa Kakansa
‘wanzami’ne, kuma tsatsonsa ba Mallawa
bane kamar yadda majiyarmu ta tabbatarwa Jaridar MADOGARA.
Sarkin Zazzau, Ahmed Nuhu Bamalli, ya tube
Ciroman Zazzau, Saidu Mailafiya mai shekara 84 a duniya bisa zarginsa da rashin
biyayya da kuma kalubalantar tsatson Sarkin.
Mailafiya, dan Sarki ne, kuma yana da
shekaru wanda ya fito daga tsatson Mallawa, tunda farkon nadin Sarkin Zazzau
din Ahmed Nuhu Bamalli, ya ki mika mubaya’a ga
sabon Sarki, sai dai daga bisani bayan bibiya da sanya baki, ya je ya mika
mubaya’arsa amma ya zare kansa daga kai ziyara a kai a kai ga sarkin bisa zargin
cewa sabon Sarkin ba tsatson Mallawa bane.
Majiyarmu ta tabbatar mana cewa; Mailafiya
ya zargi cewa sabon Sarkin na Zazzau, Ahmed Nuhu Bamalli, kakansa ‘wanzami’ ne,
wanda ya ce shi ne ma wanda ya yi masa shayi (kaciya) lokacin da yake karami.
Sai dai masana tarihi a masarautar da
littafan tarihi sun yi watsi da zargin tsohon Ciroman Zazzau din, duk da hakan
bai sanya Mailafiya ya yi watsi da zargin da ya yi ba.
Majiyarmu daga fada ta labarto mana cewa;
cire Ciroman Zazzau din bai dace, domin da Sarkin ya yi hakuri da halayyar
Ciroman Zazzau din, domin a cewarsu har mahaifin Sarkin Zazzau na yanzu wato
Nuhu Bamalli ya koma ga Allah, yana da matsala ta rashin yin biyayya da tsohon
Sarkin Zazzau Marigayi Shehu Idris.
“Marigayi
Nuhu Bamalli shima ba ya gudanar da ayyukan masarauta tun bayan mubaya’ar da ya
yi wa Marigayi Shehu Idris. Marigayi Shehu Idris ya manta da wannan matsalar,
har ya aurar da ‘yarsa ga wannan sabon sarkin wanda yake da ne ga marigayi Nuhu
Bamalli, sannan marigayi Shehu Idris ya bai wa ‘ya’yan marigayi Nuhu Bamalli guda
biyu sarauta”, majiyarmu ta tabbatar.
A wani labarin kuma, Sarkin na Zazzau,
Ahmad Nuhu Bamalli ya amince da nadin Shehu Dansidi Bamalli, Hakimin Makera a
matsayin sabon Ciroman Zazzau.
Sannan Sarkin ya amince da nadin Shehu
Mailafiya Bamalli, dan uwa ga tubabben Ciroma daga sarautar Makama Gado Da Masu
Zazzau zuwa Barden Zazzau.
Har wala yau Halliru Nuhu Bamalli shi ya
zama Makama Gado da Masu Zazzau.
No comments