Alhaji Garba Abubakar Mohammad, Sarkin Lere ta jihar Kaduna na 13 ya rasu yana da shekara 77 a duniya. Marigayin wanda ya yi gw...
Alhaji Garba Abubakar Mohammad, Sarkin Lere ta jihar Kaduna na 13 ya rasu yana da shekara 77 a duniya.
Marigayin wanda ya yi gwamnan Sakkwato a mulkin Soja, kuma ya rike shugabancin ma'aikatar kasuwanci, masana'antu, albarkatun kasa da noma ta jihar Kaduna.
An haife shi a ranar 15 ga watan Afrilun 1944 a garin Lere a jihar Kaduna. Ya kasance tsohon soja ne, kuma dan kasuwa. Ya halarci makarantar Firamarensa a Lere da Soba a shekarar 1951 da 1958 kafin ya je makarantar Barewa College Zaria daga 1959 zuwa 1963 inda ya kammala Sakandarensa.
Ya halarci Jami'ar Ahmadu Bello dake Zariya a 1965 zuwa 1966 kafin ya koma Kwalejin kimiyyah da fasaha ta 'California Polytechnic dake kasar Amurka.
Ya rasu a yau Asabar 10 ga watan Afrilun 2021.
No comments