Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar ya yi kira ga Musulmi da su koma ga Allah a daidai wannan lokacin na Ramadana. Ati...
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar ya yi kira ga Musulmi da su koma ga Allah a daidai wannan lokacin na Ramadana.
Atiku ya yi wannan kira ne a wani sakon da ya
wallafa a shafinsa na Twitter, inda a ciki ya taya al’ummar Musulmin Nijeriya
murnar shiga watan azumin Ramadana.
Sannan ya yi amfani da wannan dama wajen jan
hankali kan muhimmanci amfani da wannan watan wajen neman tuba domin ganin an
samu sauƙin matsalolin day a addabi kasarnan har ya kassarata aka kasa samun ci
gaba.
Ya kuma ƙara da cewa wannan lokaci ne na
inganta kyawawan ayyukan da kuma yawaita taimako da bada sadaka musamman ga
maɓukata.
No comments