Majalissar zartarwa ta Jihar Katsina ta amince da gyaran dokar da ta kafa hukumar kula da ilimin addinin Musulunci kamar yadda LEADERSHIP ...
Majalissar zartarwa ta Jihar Katsina ta amince da gyaran
dokar da ta kafa hukumar kula da ilimin addinin Musulunci kamar yadda
LEADERSHIP A YAU ta labarto.
Wannan zai ba da damar dora mata alhakin dubawa da
kuma kula da makarantun allo a jihar.
Mai ba gwamna shawara na musamman a kan samar da
guraben ayyukan yi Alhaji Hussaini Adamu Karadua ya bayyana haka bayan fitowa
daga taron majalissar zartarwar jiha wanda Gwamna Aminu Bello Masari ya
jagoranta.
Alhaji Hussaini Adamu Karaduwa wanda ya jagoranci
wani kwamiti na musamman domin tantance makarantun allo a jihar nan, haka kuma,
ya ce taron ya amince a mayar da almajiran da ba ‘yan asalin jihar nan ba zuwa
garuruwansu na haihuwa.
Kamar yadda ya ce daga cikin almajirai 7,893 da aka
gano, guda 2,052 sun fito ne daga jamhuriyyar Nijer, yayin da sauran ‘yan
asalin jihar Katsina ne tare da wasu da suka fito daga sauran jihohi.
Ya ce amincewa da mayar da almajiran zuwa
garuruwansu na asali da kuma yin kwaskwarima na dokar na daga cikin shawarwari
ne na kwamiti na musamman da ya jagoranta wanda aka gabatar lokacin taron
majalissar zartarwa ta jiha.
A halin da ake ciki kuma, majalisar zartarwa ta
jiha ta amince da ayyukan shawo kan zaizayar kasa da ambaliyar ruwa da zasu
lakume sama na Naira Miliyan Dubu Ukku.
Kwamishinan muhalli Alhaji Hamza Suleiman ya
tabbatar da hakan a lokacin da yake ma manema labarai jawabi bayan kammala
taron majalissar zartarwar jiha.
No comments