Jaridar Leadershi A Yau ta labarto cewa; dan takarar Gwamnan Jihar Kaduna karkashin jam’iyyar PDP a zaben shekarar 2019, Alhaji Isah Ashir...
Jaridar Leadershi A Yau ta labarto cewa; dan takarar Gwamnan Jihar Kaduna karkashin jam’iyyar PDP a zaben shekarar 2019, Alhaji Isah Ashiru ya bayyana alhininsa tare da tausaya wa wadanda suka rasa hanyoyin samun abincinsu sakamakon korar ma’aikata da Gwamnatin Jihar Kaduna karkashin jagorancin Gwamna Malam Nasiru Ahmad El- Rufa’i ta yi wanda ya ce hakan ya kara jefa dimbin jama’a cikin mawuyacin hali.
Isa Ashiru wanda kuma shi ne Sarkin Bai na Zazzau ya bayyana cewa,
kamata ya yi gwamnatinta dauki matsayin biyan ma’aikatan da ta kora a matsayin abin
da ya fi komai muhimmanci, wanda hakan zai saukaka wa iyalai da dama su samu
saukin rayuwa.
Ashiru bayyana hakan ne a cikin sanarwar da rattaba wa hannu da aka raba wa manema labarai a Kaduna, inda ya ce wadanda aka kora a halin yanzu sun shiga cikin mawuyacin hali.
Ya ci gaba da cewa, sakamakon abin da ya faru, “ina mika sakon jajantawa, alhini da tausayawa wadanda wannan lamari ya faru da su tare da iyalansu.”
Ya yi kira ga Gwamnatin Jihar Kaduna da ta shirya yadda za ta biya wadanda abin ya shafa, inda ya kara da cewa domin dukkan wani kokarin jinkiri, zai kara matsin tattalin arziki tare da kunci ne ga wadanda abin ya shafa.
Ya ci gaba da cewa al’ummar Jihar Kaduna da dukkan ‘yan Nijeriya baki daya su nan kuma su ma kallon irin abin da yake faruwa na korar ma’aikata da Gwamna El- Rufa’i ta aiwatar
Ya sanar da cewa, a yanzu dai kowa zai iya tabbatar da cewa korar ma’aikata ya zamar wa wannan gwamnatin wata manufa ce irin wadda suka kunso wa jama’a karkashin jam’iyyar APC tun da suka dare kan kujerar mulki saboda sun sallami dubban ma’aikata daga matakin jiha zuwa kananan hukumomi 23 tun a shekarar 2015 da suka kama mulki.
Ya buga misali da cewa, idan aka hada alkalumman mutanen da aka kora aiki da kuma na wadanda suka rasa harkokin kasuwancinsu, za a iya ganewa cikin sauki cewa dukkan mutanen sun shiga wani kunci domin hanyar da suke samun abincinsu duk sun zama babu don haka hadari ne babba.
Ya bayyana cewa, kamar yadda lamarin yake a halin yanzu, wadanda lamarin aikin Gwamnatin Jihar Kaduna ya shafa a dukkan fannonin rayuwa da suka hada da ma’aikatan Gwamnati, masu sana’o’in hannu da dukkan makarantan hakan, lamarin ya Jefa wasu cikin halin tsince- taince a Bola.
Ashiru ya yi nuni da cewa, lamarin ya zamanto mai Jefa kowa cikin kaduwa kasancewar Gwamnatin APC ta kasa yin amfani da ingantaccen tsarin gudanar da aikin Gwamnati da ake da shi a Jihar Kaduna domin samawa jama’a sauki,sai kawai aka yi kokarin yin amfani da tsarin da zai haifar da matsaloli da ke girgunta al’amura baki daya.
A cewarsa, irin wannan halin, yanayi da tsarin da ake tafiya ya haifarwa ma’aikata, hukumomin Gwamnati da dukkan bangarorin da daukacin kananan hukumomi durkushewa.
Ya ci gaba da cewa, kowa dai zai iya fahimtar cewa da wannan korar ma’aikatan ta kwanan nan da kuma wadda ta faru can baya, lallai alamace da ke nuni da cewa Gwamnatin, a karkashin El-Rufa’i ba ta damu da halin matsin da jama’a suke ciki ba, wanda ya bayyana a fili cewa duk lamarin ya faru ne sakamakon irin manufar da suke da shi ta tafiyar da mulki.
A karshe, Sarkin Bai na Zazzau ya ce, dukkan wata Gwamnatin da ke da tunanin halin da mutane ke ciki za ta tabbatar ta duba tare da auna dukkan abin da za ta aiwatar kafin a yi shi, domin sanin irin yadda zai zama a rayuwar al’ummar kasa, musamman a wannan lokacin da ake fama da matsalar tsaro da tattalin arziki inda da dama suka shiga cikin talauci mai tsanani da ke addabar jama’a.
No comments