Daga Hussaini Ibrahim, Gusau Kungiyar 'yan Asalin Mata ta kasa wato 'Indigenous Organization' ta ba matar gwamnan j...
Daga Hussaini Ibrahim, Gusau
Kungiyar 'yan Asalin Mata ta kasa wato 'Indigenous Organization' ta ba matar gwamnan jihar zamfara, Hajiya Aisha Bello Matawalle lambar yabo sakamakon ayyukanta na ci gaba da ta samar a Jihar ta Zamfara .
Sakatariyar yada labarai ta matar Gwamnan, Zainab Shu'aibu Abdullah ita ce ta bayyana hakan a takardar da ta sanyawa hannu ta raba wa manema labarai a Gusau babban birnin jihar Zamfara.
Zainab Shu'aibu ta bayyana cewa lambar yabon ta dogara ne da irin gudummawar da ta ke ba mata a jihar wajen inganta rayuwar mata ta kowane fanni.
Lambar yabon wacce kungiya mai suna 'Indigenous Organisation NGOs' ta bai wa matar gwamnan Zamfara, ta bata ne saboda irin gudummawar da take bayarwa tare da jajircewarta wajen bunkasa rayuwar 'yan jihar.
"Kungiyar ta baiwa Uwargidan gwamnan lambar yabon ne bisa cancanta saboda jajircewarta wajen ingantawa rayuwar mata ta fuskacin ilimi, lafiya da kuma kananan yara da taimakawa gajiyayu da masu kananan sana'oi da jari na naira 20,000.00 a kowanne wata. Kuma sama da mata 1800 ne ke amfana da wannan shirin a fadin kananan hukumomi goma sha hudu da ke cikin jihar ta Zamfara.
An zabi matar Gwamna Matawallen ne ta Zamfara tare da Matar Gwamnan Gombe, Kaduna da Kwara a matsayin wadanda suka fi cancanta da kyautatawa al'umma saboda kishin su na jihar.
"Masu bada lambar yabon suna mai da hankali kan manyan matan shugabanni waÉ—anda ke da zuciyar ci gaban Mata da matasa da yara kanana wanda sune idan rawuwarsu ta inganta al'umma ta inganta", inji ta.
Akan hakan ne Sakatariyar yada labaran, Zainab Shu'aibu Abudullahi ta jinjinawa kungiyar da kuma godiya a gareta na karrama Hajiya Aisha Matawallen Maradun domin kara mata kwarin guiwa wajen ci gaba da ayyukan da ta sa gaba na inganta rayuwar al'ummar jihar Zamfara.
No comments