Daga Muhammad Abubakar, Abuja Tsohon Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, Dakta Abubakar Bukola Saraki ya taya daukacin al’umma...
Daga Muhammad Abubakar, Abuja
Tsohon Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, Dakta Abubakar Bukola Saraki ya taya daukacin al’ummar Nijeriya da fadin duniya murnar fara azumin watan Ramadana. Ya kuma yi kira ga ‘yan Nijeriya da su yi amfani da wannan dama wurin yin addu’ar Allah Ya dawo da zaman lafiya, hadin kai da bunkasar Nijeriya.
Dakta Saraki ya bayyana haka ne a wata takardar manema labarai wacce Shugaban Sashen yada labarai naa ofishinsa, Yusuph Olaniyonu ya fitar a jiya. Ya ce, watan Ramadan lokaci ne da musulmi za su nemi kusanci ga mahaliccinsu kuma su kyautata alaka a tsakaninsu, musamman yin amfani da wannan dama wurin rokon Allah don kawo karshen zub da jini, rashin tsaro, karayar tattalin arziki da rashin hadin kan da ke addabar kasar.
“Ramadan lokaci ne na zaman lafiya. Hatta a zamanin Annabin Tsira (S) ba a yin yaki a cikin wannan wata na azumi. Yayin da muke ibada don Allah, dole ne mu tuna cewa Ramadan lokaci ne na zaman lafiya. Dalilin haka, dole ne mu yi addu’a don ganin Æ™arshen ‘yan ta’adda, ‘yan bindiga, masu garkuwa da mutane, ‘yan fashi da makami, ‘yan Ƙungiyar asiri da duk wasu nau’ikan É“arna faÉ—in Nijeriya. Haka nan kuma mu yi wa jami’an tsaronmu addu’ar samun nasara da duk wani taimako da suke bukata.
“Haka kuma, a wannan lokaci na wata mai alfarma, yana da muhimmanci waÉ—anda suke da iko da wadatar arziki su yi Æ™oÆ™ari wurin taimakawa makwabtansu da sauran raunanan dake tare da su.
“A wannan lokaci, ina son yin kira ga ‘yan kasuwa a faÉ—in Nijeriya da kada su Æ™ara farashi ga kayayyakin masarufin da ‘yan kasa ke amfani da su lokacin Ramadan. Wannan ba lokaci bane na tsawwalawa ‘yan uwanmu ‘yan Æ™asa maza da mata. Lokacin ne ma da ya kamata mu rage farashi ta yadda mutane za su iya sayan kayayyakin da su yi amfani da su a yayin sahur da buda baki.
“Ina kara yin amfani da wannan dama wurin taya ‘yan uwana musulmi murnar sake ganin zagayowar wannan wata mai girma, duk kuwa da irin matsalolin da suka addabi duniya a ‘yan watannin baya. Ina roÆ™on Allah Ya bamu yalwa da ingantacciyar lafiya don ganin Æ™arshen wannan lokaci na azumi – tare da ikon sake ganin na wasu shekaru masu zuwa.” Inji shi.
-Jaridar Tantabara Hausa
No comments