Daga Zaharaddeen Sirajo Sashen sanya ido na kungiyar kare hakkin bil'adama ta 'International Human Rights Commission (IH...
Daga Zaharaddeen Sirajo
Sashen sanya ido na kungiyar kare hakkin bil'adama ta 'International Human Rights Commission (IHRC) reshen jihar Katsina ta gudanar da taron ta na farko a ranar Lahadin 11 ga watan Afrilun 2021. Taron ya gudana ne da safiyar wannan rana da misalin karfe 10 na safe a Cibiyar 'Vocational Training Center' dake Katsina.
Taron ya gudana ne a karkashin kulawar shugaban sashen sanya ido na kungiyar ta Katsina, Ambassada Kamaludden Yahaya. Inda ya fara da fara bada tarihin kungiyar a takaice. Inda ya ce an samar da kungiyar ne domin bunkasa kare hakkin bil'adama ba tare da nuna bambanci ba. Ya kara da cewa ba nan kungiyar ta tsaya kadai ba, za ta bunkasa bangaren zaman lafiya, daidaito, lafiya, tattalin arziki da kuma wayar da kan al'umma akan 'yancin mata da kananan yara da matasa wajen bunkasa ci gaban kasa.
Ya hakkake cewa; kungiyar ta su na kare dukkanin hakkokin al'umma a fadin duniya. Tare da karfafa al'adar zama lafiya a tsakanin kasashe. "muna shawartar gwamnati da masu rike da madafun iko da su rika mutunta dokokin duniya na kare hakkin bil'adama", inji Ambassada Kamaludden.
Kungiyar ta ce; suna goyon bayan dukkanin wadanda aka zalunta da masu fafutikar kare hakkin bil'adama. "zamu bincika tare da fallasa dukkanin wanda muka kama suna take hakkin bil'adama", ya tabbatar.
Taron ya gudana ne da manufar cusawa wadanda suke bada gudummawa a tafiyar ra'ayin ci gaba da kasancewa akan turbar manufofin kungiyar.
No comments