Daga Muhammad Farouk "sakamakon shiga watan azumi na Ramadana da aka fara a yau 13 ga watan Afrilun 2021, mun zabi mu dak...
Daga Muhammad Farouk
"sakamakon shiga watan azumi na Ramadana da aka fara a yau 13 ga watan Afrilun 2021, mun zabi mu dakatar da zanga-zangarmu ta #HarassBuhariOutofLondon domin bai wa Janaral Muhammadu Buhari damar gudanar da azumisa cikin kwanciyar hankali", inji shugaban jagoran zanga-zangar neman musgunawa shugaba Buhari a Landan kamar yadda Jaridar MADOGARA ta labarto.
Ya ci gaba da cewa; "mun yi imanin cewa wannan shi ne 'yan adamtakar da zamu nuna, da kuma nuna soyayyarmu ga Allah", inji shi.
Sannan ya yi kira ga masu zanga-zangar fafutikar ganin an tsige Buhari a matsayin shugaban kasa wanda Omoyele Sowore ke jagoranta wanda Reno Omokri ya ce ba su da alaka da su ma su bi sahun matakin da suka dauka na dakatar da zanga-zangarsu domin girmama 'yan adamtaka.
Ya bayyana hakan ne a sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook a yau Talata.
Omokri ya ce za su ci gaba da sanya ido a gidan na Buhari da kuma ofisoshin likitocin da ke lura da shi idan har Janaral Muhammadu Buhari ya yi yunkurin ganin likitocin a daidai wannan lokaci, wanda suka ce idan ya yi yunkurin hakan, za su dawo su ci gaba da zanga-zangarsu domin ya karya ka'idar da suka yi.
A karshe jagoran zanga-zangar ta #HarassBuhariOutofLondon Movement, Reno Omokri ya tabbatar da cewa idan har Buhari bai karya musu ka'idarnan ba, to su za su girmama wannan wata na Musulunci mai alfarma na Ramadana ba wai saboda Buhari ba, sai saboda soyayyar da suke yi wa al'ummar Musulmi wanda suma 'Buharin ke zalunta', inji shi.
No comments