Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Pantami Zai Maka Jaridun Da Suka Alaƙanta Shi Da Ta'addanci A Kotu

Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani nq Nijeriya, Sheikh Isa Ali Pantami ya ce zai maka jaridun da suka wallafa rahotan d...


Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani nq Nijeriya, Sheikh Isa Ali Pantami ya ce zai maka jaridun da suka wallafa rahotan da ke alakanta shi da ta'ddanci a Kotu kamar yadda BBC Hausa ta nakalto. 


Sheikh Pantami ya mayar da wannan martanin ne bayan da daya daga cikin jaridun wato NewsWireNGR ta fitar da wasiƙar neman afuwan kan labarin da ta fitar da ke cewa Amurka ta sanya sunan ministan a jeren 'yan ta'adda.

Jaridar ta ce bayan ƙaddamar da bincike ta gano cewa labarin nata ba shi da tushe kuma bashi da alaƙa da Amurka don haka tana neman afuwan wanda ta ɓatawa suna da sauran masu karanta labaranta.

Jaridar ta bayyana cewa ta ɗauko labarin ne daga Daily Independent wadda ita ta soma wallafa wannan labarin.

Labarin na ikirarin cewa "Minista Pantami a baya yana yaba wa Abu Musab Al-Zarqawi a matsayin babban shugaba, wanda ya shiga ƙungiyar Al-Qaeda bayan ya yi hijira zuwa Afghanistan bayan harin da aka kai a Amurka na ranar 11 ga watan Satumbar 2001".

Batun dai ya ja hankali sosai tsakanin ƴan ƙasar musamman a shafukan sada zumunta.

Ministan dai ya ce za a haɗu a kotu domin sanin muhimmanci bincike a aikin jarida kafin wallafa kowanne irin labari.

No comments