Daga Muhammad Farouk Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani na Nijeriya, Dr Isa Ali Pantami a cikin shekarar 2006 ya taba j...
Daga Muhammad Farouk
Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani na Nijeriya, Dr Isa Ali Pantami a cikin shekarar 2006 ya taba jinjinawa jagororin Alka’ida, inda ya bayyana su a matsayin Bayin Allah tare da yi musu addu’a ta musamman a wani Jawabinsa cikin Odiyo da Jaridar MADOGARA ta samu.
Ministan a cikin jawabin ya bayyana cewa; “kuma insha Allahu muna nan akwai ranar da zamu tunkari Amerika da ikon Allah! Kuma da ikon Allah, Allah zai rugurguza su ya tabbatar da addinin Allah. Ga ‘yan’uwa da dama. Allah ya jikan Ahmad Alfadil Nazzal Al-khalayleh Rahmatullahi alaihi (daya daga cikin jagororin Alka’ida). Allah ya gafarta masa kurakuransa. Dan Adam ne yana da kura-kurai a wurin Allah, Allah ya yafe masa. Wa ke nan? Shi Abu Musab al-Zarkawi. An haife shi a shekara ta 1966, idan ka yi lissafin shekarunsa arba’in (a shekarar 2006, shekarar da aka kashe shi). Ya yi karatu na zamani a kasar Jordan. Bayan ya kammala daga nan ya yi hijira ya koma Afghanistan a wajen shekarar 1989. Ya zauna karkashin Osama bn Muhammad bn Laden, Allah ya yi masa Rahama ya gafarta masa kurakurensa. Dan Adam ne yana iya yin daidai, yana iya yin kuskure. Bayan wani lokacin shima aka ba shi na shi (sansaninsa…), Amirul muminina Mullah Omar Hafizahullahu ta’ala, ya ba shi (sansaninsa) ya bude”, ya lurantar.
Dr Ali Isa Pantami ya ci gaba da cewa; “ana farkon bayan 11 Satumba aka ji masa mummunan ciwo a kafarsa. Aka dauke shi aka kai shi Iraki ya dade yana jinya. Bayan ya gama jinya inda karshen gwagwarmayar Iraki ya zo wanda makiya Allah suka shigo cikin kasar, da ikon Allah ya tada sansaninsa suka tunkari makiya Allah. Har zuwa lokacin da cikin dare……Ya taka rawa sosai, duk da akwai wadansu abubuwa da ake nassabawa gare shi na kurakurai. Wasu na iya tabbatuwa wasu na iya yiwuwa sharri aka yi masa. Muna rokon Allah ya yafe masa. Babu kokwanto yana iya yin kuskure a ciki, domin a matsayinsa na dan Adam ba ma’asumi bane. Wannan kuma mu dauka zai iya yin kuskure. Ayyukansa na kwarai muke rokon Allah ya karba….".
"Kula da wannan a lokacin suka zo suka yi (bombing) gidan da yake ciki da wasu jama’ar da ke kewayensa su tara, aka yi ‘bombing’ dinsu. A lokacin saboda tsabar yadda ‘bomb’ din ya yi ba a ma gane jikinsu sai ‘fingerprint’ aka gane cewa shi din aka kashe. Wanda kauli ya tabbatar da cewa an kashe shi. Shiyasa kullum idan mun ji wannan maganar muna rokon Allah ya bamu ikon yin shahada. Allah yasa mu mutu karkashin gwagwarmayar addini don daukaka kalmar Allah”, inji shi.
No comments