Hukumomi a ƙasar Saudiyya da maraicen nan sun sanar da ganin watan Ramadan a yau Litinin. Hukumar Masallatai Biyu Masu Daraja na...
Hukumomi a ƙasar Saudiyya da maraicen nan sun sanar da ganin watan Ramadan a yau Litinin.
Hukumar Masallatai Biyu Masu Daraja na ƙasar wato Haramain Sharifain ce ta sanar da hakan a shafinta na Facebook.
Sanarwar na nufin a gobe Talata za a tashi da azumin Ramadana.
Tun da fari dai sai da shafin ya wallafa hoton wasu manyan malamai na ƙasar a yayin da suke duban watan gabanin Magariba.
No comments