Shugaban Majalisar Gudanarwar Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya dake Kano, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ya taya fitac...
Shugaban Majalisar Gudanarwar Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya dake Kano, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ya taya fitaccen dan jaridan nan mai daukar hoto, Muhammad Sani Maikatanga murnar lashe gasar Hotuna ta ‘Global Landscapes Forum (GLF) Africa Award’ na shekarar 2022.
Maikatanga, fitaccen dan jarida mai daukar hoto ne a Nijeriya, ya zama na farko da ya yi nasara bayan ya samu kuri'u mafi yawa. Hotonsa mai suna ‘Fishers on Run’ da aka dauka daga bikin kamun kifi na Argungu ne ya sanya ya lashe kyautar.
Sakon taya murnar na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Farfesa Abubakar Gwarzo wanda ya yi da kansa kuma aka rabawa manema labarai a Kano a ranar Talata, 14 ga watan Yuni, 2022.
An dauki hoton dubban
masuntan ne da ya samu kyauta ta dalilin hoton a yayin bikin kamun kifi na
Argungu a jihar Kebbi a shekarar 2020.
A cewarsa, ya
kamata wannan lambar yabo ta zama abin alfahari ga dukkan ‘yan jarida masu aiki
a Nijeriya musamman da ma nahiyar Afirka baki daya.
“A don haka, a
madadin Hukumar Gudanarwa ta Jami’ar Maryam Abacha American University taNijeriya
(MAAUN) dake Kano, ina taya Maikatanga murnar samun wannan nasara.
“Allah
Madaukakin Sarki ya ci gaba da ba shi karfin gwiwa da ikon yin irin wadannan
nasarori a wannan aiki nasa na daukar hoto,” in ji Farfesa Abubakar Gwarzo.
Maikatanga, dan
asalin karamar hukumar Nasarawa ne a jihar Kano, ya yi aiki da kafafen yada
labarai daban-daban na kasa da kuma na kasashen waje a matakai daban-daban.
Ya kasance dan rahoto
kuma dan jarida mai daukar hoto da Mujallar Hausa (FIM) na wasu shekaru. Ya
kuma yi aiki a matsayin É—an jarida mai É—aukar hoto mai zaman kansa tare da
jaridar Leadership sannan ya koma Media Trust Nigeria Limited, mawallafan
jaridar Daily Trust.
Ya lashe
lambobin yabo da dama a matsayin wanda ya fi daukar hoto na wata a Kamfanin Jaridar
Daily Trust baya ga karbar satifiket da kudi.
No comments