Gwamnatin Nijeriya ta shaida wa 'yan kasar cewa batutuwan da ke tare da yajin aikin da malaman jami'o'in kasar ke yi masu matu...
Gwamnatin Nijeriya ta shaida wa 'yan kasar cewa batutuwan da ke tare da yajin aikin da malaman jami'o'in kasar ke yi masu matukar sarkakiya ne.
Kungiyoyin malaman jami'a da wasu kungiyoyi uku na ma'aikatan jami'o'i sun tsunduma cikin yajin aiki, inda gwamnatin kasar ta shafe shekara tana tattaunawa da kungiyoyin domin samar da mafita, kamar yadda ministan yada labarai Lai Mohammed ya sanar.
Kungiyar malaman jami'a, ASUU ta fara yajin aiki ne daga ranar 14 ga watan Fabrairu kan wasu batutuwa da har yanzu ba a warware ba.
No comments