Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Harkar Waka Na Taka Rawa A Samar Da Zaman Lafiya, Inji Gatan Arewa

A karon farko wakilnmu Idris Umar Samaru, ya samu zantawa da matashin mawakin nan mai suna Abdulrahaman Lawal wanda aka fi sani ...


A karon farko wakilnmu Idris Umar Samaru, ya samu zantawa da matashin mawakin nan mai suna Abdulrahaman Lawal wanda aka fi sani da suna (Gatan Arewa) dan asalin jihar Kanon Dabo. 

Ga yadda zantawar ta su ta kasance kamar haka: 

Masu karatu za su so su ji takaitaccen tarihinka?

Gatan Arewa: To da farko ina mika godiyata ga Allah bayan nan ni sunana Abdulrahaman Lawal amma an fi sani na da Gatan Arewa. 

An haife ni a jihar Kano a karamar hukumar Gwammaja.

Na yi Firamare dina a Special School Gwammaja Kano kuma na yi Sakandare dina a GSS Dala jihar Kano yanzu haka ina karatu a jami'ar Ahmadu Bello Zariya.

Shin me ya baka sha'awa ka shiga harkar waka?

Gatan Arewa: gaskiya abin da ya ja hankalina ga harkar waka shi ne ganin yadda waka ke isar da sako a karamin lokaci kuma tun asalina ina sha'awar waka.

To ya zuwa yanzo ka fitar da wakoki kamar nawa kuma a cikinsu wacce kafi so?

Gatan Arewa: A gaskiya na yi wakoki masu yawa da ban san adadinsu ba amma a cikin su nafi son wakata mai suna Gatan Arewa saboda sakon dake cikinta na alheri. 

To wasu na ganin harkar waka hanya ce dake lalata tarbiya matasa me zaka ce game da lamarin?

Gatan Arewa: a gaskiya ba haka bane duk mawakin da ka ganshi ya lalace to shi ya so ya lalata kansa ba sana'ar waka ba. 

To wani shawara zaka ba masu sha'awar yin waka a zamanance?

Gatan Arewa: shawarata ga masu sha'awar yin waka a wannan zamanin shi ne su sa tsoron Allah a dukkan niyyarsu kuma su shiga harkar ba don yin kudi da sai don kawo ci gaban kasa domin waka na taimako a bangarori da yawa musamman a bangaren samun zaman lafiya tsakanin al'ummar kasa da kuma masoyi da masoyi.

To mene burinka a yanzu?

Gatan Arewa: burina shi ne na zama shahararen mawaki da kasata za ta amfana da basirar da Allah ya bani ya zamana ba za a manta da ni ba har abada a harkar waka a kasata da duniya baki daya.

To kana da sako ga mawaka 'yan'uwanka?

Gatan Arewa: Lallai ina da sako gare su; sako na shi ne mu yi kokari mu sanya natsuwa a sana'armu kuma masu dama su koma karatu domin komai da ilmi ya fi tafiya. Kuma mu zama wakilai na gari abin koyi ga al'umma kuma mu zama jakadu na kwarai a duk inda muka samu kanmu da fatan Allah ya daukakamu.

Kana da wani sako da kake so ka fadi da ba mu tambayeka ba?

Gatan Arewa: sako na shi ne ga sabuwar gwamnati ne; sakon shi ne don Allah gwamnati ta tausayawa talakan Arewa ta hanyar ba ALsu kariya ta kowanne bangare na rayuwa.

Karshe gwamnari ta rinka sanya mawaka a cikin tsarinta na kawo ci gaban kasa.

Mungode kwarai. 

Gatan Arewa: Nima na gode.

No comments