Daga Zubairu Lawal Shugabannin Jami'iyyar adawa ta PDP a jihar Nasarawa sun nesanta kansu daga zargin tsayar da wani mutum ...
Daga Zubairu Lawal
Shugabannin Jami'iyyar adawa ta PDP a jihar Nasarawa sun nesanta kansu daga zargin tsayar da wani mutum guda a matsayin ɗan takararsu a zaben 2027.
Shugabannin jam’iyyar da suka fito daga ƙananan hukumomi 13 na faɗin jihar sun bayyana cewa ba su da hannu kuma ba su amince da taro da aka gudanar a gidan tsohon shugaban jam’iyyar, Mr. Francis Orogu, a Lafia kan tsayar da Dan Takara ba.
A wata ganawa da manema labarai a zauren ’yan jarida na Lafia ranar Talata 15 ga Yuli, 2025, Comrad Jibrin Idris Ibrahim, shugaban ƙungiyar masu ruwa da tsaki na PDP a jihar, ya ce: *“Jam’iyyar PDP ba ta da wani ɗan takara guda da ta amince da shi a halin yanzu. PDP ba mallakin mutum ko ƙungiya bane; jam’iyya ce ta dimokuraɗiyya.”*
Ya bayyana cewa taron da wasu mutane suka yi a ranar 10 Yuli 2025 a gidan Orogu don tsayar da wani ɗan takara, ba shi da sahihanci kuma ba ya wakiltar ra’ayin jam’iyyar gaba ɗaya.
Ya ƙara da cewa PDP ta buɗe ƙofa ga duk masu sha’awar takara su fito, tare da kira ga kwamitin ladabtarwa na jam’iyya da ya ɗauki mataki kan Mr. Francis Orogu da sakataren yankin tsakiya da sauran masu tallata wasu ’yan takara ta hanyar da ta saba wa tsarin jam’iyya.
A ƙarshe, ya bukaci ’ya’yan jam’iyyar su zauna lafiya da juna, su girmama juna, tare da ci gaba da tattaunawa da jiga-jigan jam’iyya a shirin zaben 2027.
No comments