Daga Awwal Umar Kontagora Jam'iyyar ADC a jihar Neja ta gudanar da taron masu ruwa da tsaki da suka hada shugabannin jam...
Jam'iyyar ADC a jihar Neja ta gudanar da taron masu ruwa da tsaki da suka hada shugabannin jam'iyyar a matakin jiha da yankunan kananan hukumomi ashirin da biyar na jihar.
Tunda farko da yake amsa tambayoyin manema labarai, Alhaji Hassan Musa, yace wannan taron taro na tattaunawa tsakanin yayan jam'iyya da kuma matakan da za a bi wajen karban yan hadaka. Muna da yan takarkaru da suka yi takarar mukamai mabanbanta a zabukan da suka gabata kuma ba wanda ya fice a cikin jam'iyya, sannan har yanzu ni ne shugaban jam'iyya a matakin jiha.
Batun yan hadaka da mu, a shirye muke mu karbe su amma dole ne a bi tsarin da ya dace domin samun hadin kai da tafiya tare, bai yiwuwa za ka shiga gidan mutum ta katanga alhalin ga kofar da ake shiga gidan. Cigaba muke so, domin muna da yakinin idan aka bi kyakkyawar tsari za mu samu nasarar da muke nema.
Batun kada jam'iyya mai mulki kuwa, yau a kasar nan kowa ya ji a jikin shi, ba sai an fada ba. Saboda idan yan Nijeriya da gaske suke lokaci yayi da za mu hadaka dan ganin an kawar da wannan gwamnatin. Yan Nijeriya sun azabtu kuma a kullun gaba abin yake yi, yana da kyau masu yunkurin yin hadaka da jam'iyyar mu su bi tsarin da zai kawo hadin kai, ba bukatar kai ba, amma sun tafi suna hada sunaye da sunan ADC idan sun kammala hadawa ina zasu kai, dole ADC ta asali nan za a komo amma a daina bi ta katanga ana shirya abubuwa da sunan ADC.
Sakatariyar mu ta jiha itace wannan da ke nan Three Arm Zone kuma itace halastacciyar sakatariyar ADC inda nan muke gudanar da ayyukan jam'iyya, duk taron da ake yi da sunan ADC ba mu san da shi ba, muddin ba jam'iyya ce ta hada shi ba. Yan hadaka suna tattara kawunan su ne kuma idan lokaci yayi suka shigo ta hanyar da ya dace za mu karbe su hannu biyu, inji shugaban na jiha.
Engr. Umar Usman Maikunkele shugaban jam'iyyar ADC a karamar hukumar Bosso kuma tsohon dan takarar majalisar jiha, ya yabawa shugabancin jam'iyyar a matakin jiha, sakamakon namijin kokarin da tayi wajen hafa harsashe mai nagarta da wasu ke yunkurin shigowa dan hada hannu a fuskanci jam'iyya mai mulki.
Engr. Usman, yace ya zama yan Nijeriya su fito dan tunkarar gwamnatin nan, musamman ganin yadda matsalar tsaro, tsadar rayuwa da talauci yaci karfin al'ummar kasa. Ba za su iya ba kuma idan muka kasa fuskantar su muna zaune za a cigaba da kashe mu, ana kakabawa kasa bashi da sunan ayyukan raya kasa.
Wani aikin ne da yafi samar da ingantacciyar rayuwar da za ta kawo cigaba, zaman lafiya da hadin kan kasa, manufar mu itace hada hannu da kyakkyawar manufa na ciyar da kasa gaba.
Jam'iyyar mu tana maraba da duk wani mai kishin kasa, wanda ke son bada gudunmawa wajen ceto kasar nan daga halin da take ciki. Amma duk wanda ke da kudurin shigowa dan anfani da damar jam'iyya wajen cin bukatar kan sa, ya kwana da sanin ADC ba matsugunnin shi ba ne.
Siyasa kamar wasan kwallo, kowa na da rawar takawa dan cin ma nasara. Ina kiran yayan jam'iyya da al'ummar kasa da mu hadu mu hada hannu da kyakkyawar manufa wajen ceto kasar mu daga halin da gwamnatin nan ta jefa ta ciki.
Hon. Abdurrahman Shehu Auna, tsohon dan takarar kujerar majalisar wakilai ne a karamar hukumar Magama/Rijau. Yace tafiyar yanzu aka fara, taken mu itace hada hannu da ta hanyar musafaha da juna da kyakkyawar manufa wajen samun shugabanci da wakilci na adalci.
Tun shigowa ta jam'iyyar nan ban ga taron magoya bayan ADC ba kamar wannan taron na yau.
Wannan na nuna cewar ADC itace mafita saboda kyakkyawar tsari da manufa ta alheri ga kasar nan. Da yardar Allah kamar yadda muka jajirce a zaben da ya gabata, nan gaba ma za mu yi fiye da baya dan ganin mun samar da wakilci na gari musamman idan an yi la'akari da yadda rashin tsaro ya daidaita al'ummar mu.
Magama/Rijau, yanki ne da ya tsaya da kafarsa wajen harkar noma amma yau da daman manoman mu sun zama yan gudun hijira dole mu hada hannu dan ganin kowa ya koma gidansa dan cigaba da noma saboda samun mafitar rayuwa.
Taron dai ya samu halartar dukkanin shugabannin jam'iyyar na jiha da kananan hukumomi ashirin da biyar na jihar Neja, tare da karban sabbin yan siyasa da suka watsar da jam'iyyunsu dan hada hannu da ADC dan fuskantar shekarar 2027.
No comments