Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Shekara ɗaya da hawan sa sarauta, Olubadan na Ibadan, Oba Olakulehin ya mutu yana da shekara 90

Olubadan na Ibadanland, Oba Owolabi Olakulehin, ya koma ga mahaliccinsa. Jaridar Tribune Online ta rawaito cewa, basaraken wanda ya hau kara...


Olubadan na Ibadanland, Oba Owolabi Olakulehin, ya koma ga mahaliccinsa.

Jaridar Tribune Online ta rawaito cewa, basaraken wanda ya hau karagar mulki a watan Yulin 2024, ya rasu a safiyar Litinin, 7 ga Yuli, 2025, bayan shekara guda kacal da hawansa karagar mulki.

Rasuwar Oba Olakulehin, wanda aka haifa a ranar 5 ga Yuli, 1935, ta zo ne kwanaki biyu bayan bikin zagayowar ranar haihuwarsa ta shekaru 90.

Tribune Online ta bayyana cewa Oba Olakulehin ya karɓi sandar mulki daga Gwamnan Jihar Oyo, Injiniya Seyi Makinde, a ranar 12 ga Yuli, 2024, a matsayin Olubadan na Ibadan na 43.

Oba Olakulehin ya hau karagar mulki ne daga matakin sarauta na Balogun Olubadan, bayan rasuwar Oba (Dr.) Moshood Lekan Balogun, Alli Okunmade II, wanda ya rasu yana da shekaru 81 a ranar 14 ga Maris, 2024.

No comments