Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Makon Qur'ani: Kungiyar Mahaddata Sun Gudanar Da Addu'o'i Na Musamman A Minna

Daga Awwal Umar Kontagora Cibiyar mahaddata Alkur'ani ta Nijeriya wacce aka fi sani da 'Center for Qur'anic reciters of Nigeria...


Daga Awwal Umar Kontagora

Cibiyar mahaddata Alkur'ani ta Nijeriya wacce aka fi sani da 'Center for Qur'anic reciters of Nigeria' a turance bisa jagoorancin Sheikh Hassan Musa ta shirya saukar Alkur'ani mai tsalki da gudanar da addu'o'i na musamman kan halin rashin tsato, fatara da tsadar rayuwa da addabi kasar nan.

Tunda farko bayan amsa tambayoyin manema labarai lahadin makon nan da kungiyar ke kammala addu'o'in kwana uku da aka fara ranar juma'a zuwa lahadi. Shugaban kungiyar ta kasa, yace tun farko shi jagoranci assasa kungiyar bisa goyon bayan marigayi Sheikh Isyaka Rabi'u. Wanda tun bayan kafuwar kungiyar ta taka rawar gani wajen hada kan malaman tsangayu, alarammomi da maau neman sanin Alkur'ani mai tsalki, wanda hakan ya taimaka gaya wajen samun cigaban makarantun tsangayu.

Sheikh Hassan ya cigaba da cewar dalilin shirya wannan taron addu'o'in da ya kunshi jahohi goma sha tara na arewacin kasar nan, shi don neman kusanci ga Allah da rokonsa kan halin al'ummar kasar nan ke ciki na tashin hankula akan rashin tsaro, fatara da kuncin rayuwar da al'umma ke ciki.

" Lallai gwamnati na bakin kokarinta amma a kullun matsalolin karuwa suke, sai muka ga dacewar bayan addu'o'in da muke gabatarwa a makarantun tsangayun mu da mu nemi juna dan shirya wannan addu'ar da mu ka yiwa lakabi da Makon Alkur'ani.

Manyan limamai da malamai sun halarci wannan taron da muke kammalawa yau daga sassan jahohin arewacin kasar nan goma sha tara.

Da yake karin haske, Gwani Salisu Mohammed, mataimakin shugaban kungiyar Huffazul Qut'an rrshen jihar Neja, yace ya zama wajibi mu ajiye bambance bambancen da ke tsakanin wajen fuskantar matsalolin da ke damun mu

Yau iyaye sun watsar da nauyin da ke kan su na kulawa da tarbiyar yayansu, shugabanni sun watsar da amanar kulawa da hakkokan da ke kan su. Kuma idan matsaloli sun yi yawa babu abinda ke walwale su face komawa ga Allah

Na yabawa jagorancin Sheikh Hassan Musa duk da halin da ake ciki ya shirya wannan taron kuma muna fatar Allah ya amsho addu',o'in da aka gabatar.

Gwani Abdulkadir Muhammad Barkum, kuma babban limamin masallacin juma'ar Rangaza da ke karamar hukumar Ungogo ta jihar Kano, ya bayyana cewar tun farko an yi sake ne, domin Allah mai ji ne kuma mai gani, duk lokacin da matsaloli suka taso aka kusanci Allah da kyakkyawar niyyah, musamman aka karanta Alkur'ani mai tsalki aka yi addu'a za a samu mafita, domin Alkur'anin nan shi ne mafita ga al'umma.

Gwani Comr. Umar Ahmed Muhammad Na Milli kuma amai Dan Majen Gumel, ya nemi dukkanin kungiyoyin mahaddata da su hada kai wuri daya su kawar da kwadayi da son shugabanci su yiwa Alkur'ani hidima, lallai za a samu cigaban da ba a yi tsammani ba.

Yace yanzu haka saboda irin wannan namijin aikin na hada kai da muka sanya a gaba, akwai littafin da muke rubutawa wanda muna gab kaddamar da shi domin hadin kan sarakuna iyayen kasa da fuskantar matsalolin da rarrabuwa kawuna da ya janyowa al'ummar koma baya.

Dan Majen, wanda shi ne wakilin masu sarautun gargajiya wanda kuma mahaddaci Alkur'ani mai tsalki ne, ya yabawa sarakunan jihar Neja, bisa goyon bayan da suke baiwa malamai, musamman mai martaba sarkin Minna, Dakta Umar Faruq Bahago da ya zama mai bada shawarwari nagartattu a kowani lokaci.

Mafi yawan abinda ke kawo rarrabuwan kawuna abu biyu ne, son shugabanci da neman kudi. A jagorancin da Allah ya ba mu na wakiltar masu rawunan gargajiya mu kan jibintar da duk wani abinda ya alakanta ga kudi saboda kare mutuncin shugabancin da al'umma suka ba mu. Kuma za mu tabbatar a kowani lokaci mun baiwa al'umma damar sanin duk wani abu da ke shigowa na tafiyar da jagorancin da. suka ba mu.

Imam Nura Malami, limamin masallacin juma'ar Imam Malik da ke Fly-over cikin garin Sokoto kuwa, kira yayi ga Malamai da su hada kai su kawar da duk wani bambance bambance duk manufar mu daya ce wato Alkur'ani mai tsalki, kuma idan har Sheikh Hassan Musa zai yi irin wannan gagarumin aikin na hada kan malamai dan tsayuwa akan manufa daya wato fuskantar matsalolin da al'ummar kasar nan ke ciki da kuma neman hanyar walwale su, lallai abu ne da ke bukatar goyon baya sosai

Yau idan ka dubi halin da jahohin Sokoto, Kebbi, Zamfara da Neja ke ciki wajibi mu yi gaggawar dauki ta hanyar riko da Alkur'ani mai tsalki.

Mun zabi jihar Neja ne ta zamo za a gudanar da wannan taron na kasa, kasancewar tana cikin jahohin da ke fuskantar wannan matsalar tsaron, kuma a wannan jihar shugaban kungiya na kasa ya fito.

Wannan turbar da kunggiyar nan ta dauka ita kadai ce ta rage mana a. yanzu. Domin a matsayin mu nna musulmi muna da yakinin duk lokacin da wata fitina ta auku idan aka koma ga Allah. za a samu mafita.

A matsayina na sakataren tsare ttsare muka tsari cigaba da shirya irin wannan taron addu',o'in lokaci zuwa lokaci

Da yake jawabi a taron, jami'in yada labarai na jam'iyyar APC mai mulki, Hon. Labaran Sarkin Kaji, ya yabawa kungiyar kan shirya wannan taron, inda ya bayyana cewar taron addu',o',in yazo akan gaba musamman duk da irin namijin kokarin da gwamnatin tarayya da ta jihar Neja bisa jagorancin babban manomin jiha, Dakta Umaru Mohamned Bago ke yi yan ta'adda na cigaba yiwa tsaro barazana.

Amma gwamnati na da kwarin guiwar tsayuwar malamai akan kusanci da Allah, tabbas za a samu gagarumin nasara wajen murkushe ta'addanci da yan ta'adda a jihar Neja da kasa baki daya. 


No comments