Daga Awwal Umar Kontagora An nemi masu hannu da shuni da sauran al'umma da su kula da tarbiyar yayansu dan samun baya na kwarai da zasu ...
Daga Awwal Umar Kontagora
An nemi masu hannu da shuni da sauran al'umma da su kula da tarbiyar yayansu dan samun baya na kwarai da zasu rika yiwa iyayen si addu'a idan sun yi wafati. Alhaji Sulaiman Yahaya Babangida ( Cikasoron Minna kuma Barde Kerarriyar Agaie) ne yayi kiran a lokacin da yake jawabi lokacin gabatar da addu'o'in cika shekaru biyar da rasuwar mahaifiyarsa,Marigayiya Hajiya Fatima ( Inna) da babban limamin masallacin juma'ar Minna ya jagoranta tare da sauran manyan limamin juma'a da shugabannin addinin musuluncia jihar Neja.
Cikasoro ya cigaba da cewar rashin mahaifa rashi babba da ba za a iya cike gurbinsa ba. Babu wani abu mafi alkhairi da mutum zai mutu ya bari ya cigaba da wanzu kamar ayyukan alkhairi da samun yayan na gari wadanda zasu rika gabatar da ayyukan alkhairi da nufin ladarya isa wurin mahaifa ko yawaita yi masu addu'o'i dan samun rahamar Allah.
Alhaji Sulaiman ya cigaba da cewar ba hujja ba ne mutum ya haifi yaya sannan ya sanya idanu suna ayyukan da ba su dace ba, yayi tsammanin wani ko gwamnati ce za ta kula masa da tarbiyar yayansa.
Abin bakin ciki da takaici ne ganin yadda tarbiyar matasa ya sukurkuce suka koma daukar makamai da sunan sara suka, sace sace da aukawa al'umma kuma a hakan ake tsammanin su zama mutanen kirki a gaba. Ya zama wajibi a matakin farko uba ya kula da ciyarwa da suturtarwa gami da bada ilimin addini da na zamani da koyar da su sana'o'i idan sun kai munzalin koyon sana'a.
Tarbiya itace ginin farko da ake yiwa yaya, sannan ilimi kafin sana'a ya biyo baya,wanda hakan zai sa kowani lokaci idan yaro ya juya bai ga mahaifansa ba yayi masu addu'a ko samar da wani abu nai anfani da al'umma zasu anfana da nufin kai lada gurin mahaifansa.
Tunda farko a bayaninsa, shugaban kungiyar Huffazul Qur'an and Islamic Scholars Association reshen jihar Neja, Gwani Sheikh Hussaini Abubakar Shakwata ya bayyana cewar abinda ake nema idan aka kyautata niyya aka rungumi Al-qur'ani za a same shi. Yanzu alarammomi sun jagoranci saukar Al-qur'ani mai tsalki, kuma manyan malamai sun jagoranci addu'o'i da nufin neman lada da rahamar Allah ga wannan baiwar Allah Hajiya Fatima mahaifiyar Cikasoro wannan abu ne mai kyau kuma yana da asali a addini.
Dan haka kamar yadda malumma suka bayyana cewar babu wani aikin alkhairi mafi soyuwa a gurin Allah kamar karanta Al-qur'ani mai tsalki da nufin neman yardar Allah.
Sannan gina rijiya ko makaranta ko wani aikin alkkhairi ayi bakance da shi dan neman yardarAllah.
Barista Sheikh Muhammad Salisu Maidala'ilu babban limamin masallacin juma'ar Tunga da ke Minna, cewa yayi Al-qur'ani waraka ce idan an kyautata niyya aka karanta shi, ba abinda A a nema Allah bai bbbada shi ba idan an yi hakuri.
Saboda haka, akwai bukatar iyaye su koyi da irin wannan aikin na daukar nauyin yiwa iyaye addu'a. Domin barin yaya ba Al-qur'ani shi ne. ya jefa yara matasa ga ayyukan ddda ba su dace ba, tun wuri mu farka daga dogon baccin da muke yi, yana daga cikin abinda muka assasa kowani limamin hamsis salawati da ya cigaba da fadakar da iyaye muhimmancin kulawar tarbiya da ilmantatwa ga yayan su.
Yau yaran nan kannan mu ne, yayan mu ne idan muka sanya idanu muka bar su a wannan yanayin tabbas al'umma za ta cigaba da fuskantar matsalolin rayuwa na tashe tadhen hankula sakamakon abinda matasan suka janyo mana.
Malamin ya yabawa Cikasoro na shirya wannan babban taron na alarammomi tare da malamai dan yiwa mahaifiyarsa addu'a.
An dai raba Al-qur'anai a matsayin kyauta ta musamman ga malamai, limamai da alarammomin da suka halarci addu'o'in.
Tsohon kwamishinan ayyuka a jihar Neja kuma tsohon ministan wasanni Injiniya Sani Ndanusa ( Marafan Bida) shi shugabanci taron.
No comments