Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamna Bago Ya Fahimci Masu Yi Wa Gwamnatinsa Zagon Kasa Ya Fuskanci Ayyukan Raya Kasa - Yanga

Daga Awwal Umar Kontagora An yi kira ga gwamnan jihar Neja da ya mayar da hankalinsa kan ayyukan raya kasa da sanya a gaba,  ya kawar da kai...


Daga Awwal Umar Kontagora

An yi kira ga gwamnan jihar Neja da ya mayar da hankalinsa kan ayyukan raya kasa da sanya a gaba,  ya kawar da kai kan masu yunkurin yiwa gwamnatinsa zagon kasa, domin rajin yayata takarar shugaban kasa ga gwamnan a shekarar 2027 ba wani abu suke kullawa ba face kawo sabani tsakaninsa da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.

Wani jigo a jam'iyyar APC a karamar hukumar Chanchaga,  Allhaji Hamza Yanga Buba ne yayi kiran yammacin asabar din makon nan a Minna.

Yanga Buba, ya cigaba da cewar wadannan mutanen ba wani abu suke haddasawa ba face gurgunta ayyukan da gwamnatin Neja ta sanyo a gaba ba, domin sun saba so yi kwance and kawo masu kudaden gwamnati suna ci,  a wannan karon ba su samu irin wannan rashin suna kwasa ba yasa suke kulle kullen haddasa rikici tsakanin gwamna da shugaban kasa ba.

Taya gwamnatin da ba ta wuce shekaru biyu akan mulki ba, kuma a zangon farko ake mata kallon zarcewa zuwa fadar shugaban kasa kuma a jam'iyya daya,  da walakin goro a miya,  kawai wani yunkuri ne na ingiza mai kantu,  su sani an yi walkiya mun gan su, kamar yadda gwamna Bago ya dauko wadannan muhimman ayyukan da hannunsa zai kammala su.

Saboda haka,  ina kira ga al'ummar Neja da su cigaba da baiwa gwamnatin Ahmed Bola Tinubu da Umaru Bago goyon baya,  su daina bin yan tayi ruwa rijiya domin ba su da kudurin da ya wuce tabare, cikin shekaru biyu kacal mun ga ayyukan da wadanda suka shekara takwas ba su yi ba.

Mu halattatun yan APC ne kuma mun gamsu da kamun madafun ikon da ke jagoranci yanzu. Za mu cigaba I da fitowa dan kare mutuncin gwamnati mai ci dan mun shaida ayyukan da ta sanya a gaba mai anfani ne,  ayyuka ne na dawn da martabar jihar mu, da yayan mu zasu yi alfaharin cewar ba mu yi zaben tumun dare ba.

Kamar yadda muke fatar shugaba Tinubu yayi shekaru takwas haka muke fatar Umaru Mohammed Bago yayi takwas kan karagar mulkin jihar nan. 


No comments