Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Bamu Kafa ‘June 12’ Don Cin Zarafin Wani Sashen Al’umma Ba - Wana

Daga Awwal Umar Kontagora An bayyana cewar wadanda suka kafa tafiyar June 12 ba sun kafa shi ba ne dan yin anfani da su wajen cin zarafin wa...


Daga Awwal Umar Kontagora

An bayyana cewar wadanda suka kafa tafiyar June 12 ba sun kafa shi ba ne dan yin anfani da su wajen cin zarafin wani ko wani sashin kasar nan ba,  mun kafa tafiyar dan sanin hakikanin abinda ya janyo rushe zaben da ake gab da kammalawa a lokacin,  hakan kuma bai hana gwamnatin soja na lokacin cin zarafin mu tare da daure wasun mu shekaru dari zuwa dari uku a kurkuku ba,  amma Allah cikin ikonsa bai ba su damar cin ma mummunar kudurinsu akan mu ba.

Tsohon sakataren jam'iyyar NPP a lokacin kuma daya daga cikin mutane ashirin da uku da suka assasa tafiyar June 12 kuma daya daga cikin dattijan da suka marawa takarar Bola Ahmed Tinubu a zaben 2023, Alhaji Awaisu Giwa Wana ne ya bayyana hakan a lokacin bukin ranar dimukuradiyya da ya gudana tsakiyar makon nan mai karewa.

Awaisu Wana,  ya cigaba da cewar koda tsohon shugaban kasa,  Muhammadu Buhari ya mayar da June 12 matsayin ranar dimukuradiyya a kasar nan,  wani gudunmawa ya baiwa dimukuradiyyar, alhalin in ma laifi ne ko cin amanar dimukuradiyya ne yake zargin Janar Ibrahim Badamasi Babangida ne,  laifin Buharin yafi na Babangida, domin Janar Buhari shi ya kifar da zababbiyar gwamnatin dimukuradiyya ta marigayi Alhaji Shehu Shagari kuma har yau Janar Buhari ba zai iya fadawa yan Nijeriya inda ya salwantar da makuddan kudade da kaddarorin da ya karbo hannun yan siyasar lokacin ba.

Kuskuren shugaba Tinubu a wannan bagiren yace zai yiwa yan kasa bayani kan cigaban da aka samu game da mulkinsa,  amma sai ya buge da bada lambar yabo wanda ba mu taba gani a siyasar duniya an gayyato shugabannin majalisar dokokin kasa ana bada lambar yabo ba, abinda yan Nijeriya ke bukata shi ne sanin inda aka kwana akan matsalar tsaro, tabarbarewar tattalin arzikin kasa da tsadar rayuwar da suke fama da shi.

Idan ma shugaban kasa wani abin yake kullawa da shugabannin majalisa, to ya sani talakawan nan da suka yi zabe suna jiran shi. Maganar hadin kan kasa, ba wannan hanyar da ake akai yanzu ya kamata abi,  domin tsarin dokokin kasar gurbi uku ne ke tafiyar da shi, bangaren zartaswa, majalisa da alkalai. Ko yan majalisa da ke yekuwar sahalewa shugaban kasa zango na biyu ba wani abinda zasu iya yi mai idan zabe yazo.

In har da gaske ne ana neman walwale matsalolin kasar nan,  dayan uku ya kamata yi, kiran kasa da zai baiwa kowa damar fadin albarkacin bakin shi, ko kuma hukumar zabe ta kasa mai zaman kan ta kamar yadda ake cewa ta shirya taron jin ra'ayin jama'a dan har yanzu akwai al'ummomi da dama da ba su san ana dimukuradiyya ba,  ko kuma a kira taron rafamdum na kasa baki daya. Kuma a tabbatar an aiwatar da abinda aka tattauna hakan kawai zai fitar da wasi-wasi a zukatan al'ummar kasar nan kan zargin bangaranci da nuna fifikon da ake yi wajen raba mukaman siyasa a kasar nan.

Dangane da wadanda aka karrama ina taya su murna musamman wadanda ke raye irin su Kwamred Shehu Sani da muka yi gwagwarmayar June 12 da makamantan su. Amma maganar gaskiya indai da irin wannan salon siyasar ake tsammanin samun nasara a zaben 2027 to a canja tunani domin ba lallai a samu abinda ake bukata ba. 


No comments