Farfesa Gwarzo Ya Samu Lambar Karramawa A Faransa, Wakilin UNESCO Ya Halarta Jami’ar Cité Universitaire de Paris , daya daga cikin fitatt...
Farfesa Gwarzo Ya Samu Lambar Karramawa A Faransa, Wakilin UNESCO Ya
Halarta
Jami’ar Cité Universitaire de Paris,
daya daga cikin fitattun jami’o’i a Faransa da ake darajawa, wacce ke matsayi
na 12 a fadin Turai, ta karrama Farfesa
Adamu Abubakar Gwarzo, Shugaban Ƙungiyar Jami’o’i Masu Zaman Kansu na
Afirka (AAPU), da Lambar Girmamawa mai
daraja saboda gudunmawar sa wajen bunkasa ilimi a Afirka da ma duniya
baki É—aya.
An mika lambar yabon ne a ranar Juma’a, 13 ga watan Yuni, 2025, ta hannun
Shugaban Jami’ar, Sanata Jean Mac Sauve,
inda aka gudanar da bikin a matsayin wani bangare na shagulgulan cika shekaru 100 da kafuwar jami’ar, da
kuma wani taron kasa da kasa kan bunkasa
ilimi da bincike a Afirka.
Taron ya samu halartar manyan masana daga
jami’o’i daban-daban na duniya. A jawabinsa, Sanata Jean Mac Sauve ya bayyana jin daÉ—insa da irin
rawar da Farfesa Gwarzo ke takawa wajen wakiltar Faransa cikin kima a Afirka,
kasancewar sa É—an tsohuwar makarantar ta Faransa.
Ya yabawa Farfesa Gwarzo kan yadda yake zuba
hannun jari a bangaren ilimi tare da sadaukarwar da yake yi wajen bunkasa
manyan makarantu a Nijeriya da Afirka baki daya, yana mai cewa hakan abin yabo
ne matuƙa.
Wakiliyar Dindindin ta Nijeriya a UNESCO, Jakadiya Dr. Hajo Sani, ita ce ta
wakilci Nijeriya a wajen bikin, inda ta yabawa jami’ar bisa zaÉ“ar Farfesa
Gwarzo a matsayin wanda ya cancanci wannan girmamawa. Ta ce wannan yabo babbar
shaida ce kan jajircewar Farfesan wajen ci gaban ilimi da tasirinsa ga al’ummar
ilimi gaba É—aya.
Jakadiya Hajo Sani ta kara da cewa Farfesa
Gwarzo ya ba da gudunmawa sosan gaske kuma mai tsoka ta hanyar kafa jami’o’i
guda uku a Nijeriya, inda ta bayyana cewa har ‘ya’yanta biyu suna daga cikin
waÉ—anda ke cin moriyar wannan gagarumin ci gaba.
A nasa bangaren, Farfesa Gwarzo ya nuna godiya ga jami’ar ta Faransa bisa
wannan lambar girmamawa da aka ba shi, yana mai nanata kudurinsa na ci gaba da
inganta harkar ilimi ba kawai a Afirka ba, har ma a duniya baki É—aya.
Ya kuma yi kira ga dukkan ‘yan Afirka da ke
karatu a ƙasashen waje da su dawo gida bayan kammala karatu, domin ba da
gudunmawa wajen gina nahiyar Afirka da har yanzu ke da buƙatar ci gaba.
A karshe, Farfesa Gwarzo ya ce wannan lambar
yabo za ta Æ™ara masa Æ™warin gwiwa wajen ci gaba da jagorantar gamayyar jami’o’in
MAAUN zuwa ga samar da ingantaccen ilimi mai tasiri ga ci
gaban rayuwar al’umma.
Lambar
Girmamawar ta zama wata kwakkwarar shaida ta irin tasiri da sadaukarwar Farfesa
Gwarzo wajen haɓaka ilimi a matakin duniya.
No comments