Daga Idris Umar Shugaban ƙaramar hukumar Sabon Gari kuma shugaban ƙungiyar shugabannin ƙananan hukumomi na jihar Kaduna (ALGON),...
Daga Idris Umar
Shugaban ƙaramar hukumar Sabon Gari kuma shugaban ƙungiyar shugabannin ƙananan hukumomi na jihar Kaduna (ALGON), Honorabul Sheikh Muhammad Jamilu Abubakar Albani Samaru, ya bayar da tallafin kuɗi ga ɗalibai wanda suke matakin digiri na biyu wato 'mastas' ga ƴan ƙaramar hukumar Sabon Gari don cigaban karatunsu. Adadin kuɗin ya kai miliyan ɗaya da dubu ɗari biyu ga ɗalibai goma sha biyu.
Taron an gudanar da shi ne a babban ɗakin taro na Sakatariyar ƙaramar hukumar dake Dogarawa, Honorabul Jamilu Abubakar ya bayyana cewa, wannan tallafi ya biyo bayan nazari ne da suka yi don karfafa harkokin ilmi a ƙaramar hukumar ta sabon Gari da jihar Kaduna baki ɗaya.
Ya jaddada cewa gwamnatin Gwamna Uba Sani gwamnati ce mai tausayi da adalci, kuma hakan ne ya sanya su ɗaukar matakin tallafa wa waannan Ɗalibai domin rage musu raɗaɗin matsin rayuwa. A cewarsa, an ware Naira Miliyan ɗaya a matsayin tallafi ga ɗaliban.
Bayan miƙa tallafin, shugaban Ɗaliban Kwamared Jibirin Salihi, ya nuna godiyarsa tare da ɗaukar alƙawarin cewa za su mara wa jam'iyyar APC baya a dukkan matakai, bisa irin kulawar da suka samu daga gwamnatin jihar Kaduna ƙarƙashin Gwamnan Sanata Uba Sani da shugaban ƙaramar hukumar Sabon Garin Honorabul Abubakar Jamilu Albani.
Taron ya samu halartar manyan baƙi ciki har da mataimakin shugaban ƙaramar hukumar, Hon. Kamilu Abdul-Kareem, da Hon. Sani Jibirin Chikaji, tare da sauran masu ruwa da tsaki.
A ƙarshe, malamai da limamai sun sanya albarka ga shugaban ƙaramar hukumar bisa irin ƙoƙari da jajircewar da yake nunawa wajen kawo ci gaba a Sabon Gari.
No comments