Daga Awwal Umar Kontagora Jam'iyyar ADC (African Democratic Congress) ta sha alwashin samar da shugabanci na gari a jihar Neja. Shugaba...
Daga Awwal Umar Kontagora
Jam'iyyar ADC (African Democratic Congress) ta sha alwashin samar da shugabanci na gari a jihar Neja. Shugaban Jam'iyyar Alhaji Musa Hassan ne ya bada tabbacin lokacin bude sakatariyar jam'iyyar ta jiha da na shiyya da ya gudana cikin makon nan ga manana labarai.
Shugaban ya cigaba da cewar aza harsashin tafiyar jam'iyyar zai tabbatar da hadin Kai, cigaba da samar da sabuwar tafiyar siyasa a kasa baki daya. Hakan na nufin kyautata niyya da yin aiki tukuru ga yayan jam'iyya domin yin imani da tsare tsaren jam'iyya wadanda suka yi imanin bautawa kasa, kiyaye dukiyar kasa, cigaban al'umma, ta hanyar hada hannu dan yin aiki tare.
Haduwar mu ayau, ya shafi dukkan masu ruwa da tsaki daga dukkan bangarorin siyasa, da kuma kwararrun shugabanni, kungiyoyin matasa, kungiyoyin mata, da wakilan al'umma wadanda ke da kyakkyawar fata wajen samun sabuwar tsarin siyasar gina kasa ta hanyar hada hannu da kwararrun shugabanci.
A bayaninsa, shugaban jam'iyyar reshen arewa ta tsakiya, Dakta Peter Edeh ya bayyana cewar aikin gina kasa ya dogara ne wajen kawar da yunwa, samar da tsaron rayuka da dukiyoyin al'umma. Idan an koma kan irin tsarin tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida tsarin ne na yaki da fatara, ayyukan cigaban kasa wanda sanin kowa an samu gagarumin nasara a lokacin sabanin tsarin da ake tafiyar shugabancin kasar nan ayau da sunan cigaba .
Ana kashe al'umma , an kakabawa al'umma yunwa ana kwasar dukiyar kasa ba tare da la'akari da halin da kasa ke ciki ba. Taken mu hada hannu dan yin aiki tare akan matsalolin da kasa ke ciki.
Alhaji Sa'id Baba Abdullahi, shi ne sakataren jam'iyyar ta kasa kuma wakilin shugaban jam'iyyar ta kasa, Chief Raph Okay Nwoso, yace hada hannu wajen gina kasa da fuskantar matsalolin kasar nan shi ne a gaban su. Kamar yadda wasu yayan jam'iyyu suka amince da manufofin jam'iyyar ADC suka yarda a hada hannu dan dunkulewa waje daya saboda ceto kasar nan daga halin da take ciki ayau, wannan ya nuna damba aka sanya dan fuskantar zabukan 2027 mai zuwa.
Saboda haka kofar mu a bude take ga duk mai kaunar wanzuwar dimukuradiyya a kasar nan, saboda mu hada hannu dan yin aiki tare.
Jam'iyyar ADC ba sabuwar jam'iyyar ba ce domin ta kwashe shekaru sama da ashirin tana taka rawar gani a siyasar kasar nan. Kan haka ta shiga sahun farko a jam'iyyun da ake fafatawa da su a manyan zabukan kasar nan.
Bayan bude sakatariyoyin jam'iyyar guda biyu, jam'iyyar ta karbi yayan wasu jam'iyyu da suka -canja sheka dan yin tafiya tare. Taron dai ya gudana ne a sabon sakatariyar jam'iyyar ta jiha da ke rukunin Nagari Residential Layout da ke Minna.
No comments