Daga Awwal Umar Kontagora Qungiyar Huffazul Qur'an and Islamic Scholars ta tallafawa malamin tsangayar da iftila'in ruwan Mokwa yayi...
Daga Awwal Umar Kontagora
Qungiyar Huffazul Qur'an and Islamic Scholars ta tallafawa malamin tsangayar da iftila'in ruwan Mokwa yayi sanadin mutuwar almajiransa takwas.
Tunda farko a bayaninsa, shugaban kungiyar a jihar Neja, Gwani Sheikh Hussaini Abubakar Shakwata, ya bayyana cewar samun wannan mummunar labarin da ya shafi almajiran Al-qur'ani mai tsalki, ya kada sosai, wanda wannan ba karamin hasara ba ne ga al'umma.
Gwani Hussaini Shakwata, ya jawo hankalin gwamnati da masu ruwa da tsaki da su dauki matakin gaggawa wajen kaucewa faruwar irin wannan a gaba.
Kungiuar dai ta tallafawa malamin da naira dubu dari da saba"in da biyu dan yin anfani da kudin wajen cigaba da kulawa da marasa lafiya, da kuma samun damar sayen abinci ga sauran iyalai.
Malam Hassan Umar Mokwa, malamin da iftila'in anbaliyar ya shafi almajiran sa, ya yabawa gwamnati jihar Neja da sauran kungiyoyi masu zaman kan su musamman ita kungiyar Huffazu da suke ta dawainiya da bada gudunmawa kan al'umma da wannan iftila'in ya shafa.
Malamin, ya cigaba da cewar tsangayar mu akwai almajirai dari takwas da doriya ,lokacin da abin ya faru mun yi kokarin tantance almajiran mu. Da farko bincike ya nuna mana mutane shida ne suka rasu amma yau mun samu karin mutum biyu.
Wasu iyayen sun kwashe yayansu saboda fargaba, amma yanzu sama da dari biyu sun dawo.
Malamin yace ina da shekaru hamsin da shida da haihuwa kuma a nan garin Mokwa yankin da iftila'in ya auku aka haife ni ban taba ganin irin wannan yanayin ba sai wannan karon.
Muna neman tallafin gwamnati wajen sake assasa wannan tsangayar musamman tunda maigirma gwamna yayi alkawalin tallafa mana, abinda aka samu a ba mu kudaden a hannu samun damar sayen wani gurin dan gina tsangayoyin mu dan mu cigaba da karatu.
No comments