Daga Awwal Umar Kontagora Wani matashi kuma jigo a jam'iyyar APC a jihar Neja yayi kira ga jam'iyyar APC da ta guji kawo rarrabuwar ...
Daga Awwal Umar Kontagora
Wani matashi kuma jigo a jam'iyyar APC a jihar Neja yayi kira ga jam'iyyar APC da ta guji kawo rarrabuwar kawuna tsakanin yayan jam'iyya. Hon. Zakari Mohammed Kuchi ne yayi kiran a Minna fadar gwamnatin Neja.
Dan siyasar yace maganar 2027 yayi wuri a ce an fara kamfe tun yanzu, gwamnati ba ta wuce shekaru biyu da kafuwa ba, kuma da daman yayan jam'iyya ba su san makonarsu ba, ya kamata ne yanzu jam'iyya ta samar da hadin kai tsakanin yayanta ba wai maganar yakin neman zabe mai zuwa ba.
Ya kamata ne mu dauki darasi akan jam'iyyar PDP da tai shekaru goma sha shida wanda matsalolin cikin gida ya kawar da ita akan madafun iko ba tare da wahala ba, mutane sun wa jam'iyya aiki ba tare da samun humusi ba, kuma ba a ma nuna masu jinjina akan aikin da su ka yi ba, balle su fahimci cewar an yabawa ayyukan da suka yi.
Ya kamata gwamnonin jahohin APC da yan majalisun da ke muradin cigaba da siyasa, zukatan su ya zama al'ummarsu farko ba bukatun kan su ba, amma irin tafiyar da ake yi yanzu idan ba a yi hankali ba akwai matsala a gaba.
Dangane da batun da ya dabaibaye siyasar APC kan matsayin mataimakin shugaban kasa kuwa, kan maganganun gwamnan Barno, Umara Zulum da batun baiwa shugaban jam'iyya ta kasa kuwa, ya kamata abi a hankali domin duk da cewar yana wa'adin karshe ne kan kujerar gwamna, jam'iyya ba da bukatarsa domin jama'ar da yake mulki suna tare da shi saboda irin gudumawar da yake baiwa jiharsa sannan wanda ake batu ubangidansa ne kuma suna da karfi a siyasar arewa ta gabas duk da halin rashin tsaro da yankin ke fuskanta.
Ya zama wajibi shugabanni su yi gyara akan kurakuran da aka yi a baya, mu ajiye bambamcin addini, shiyya da yare ayi raba daidai ta yadda za a kauracewa zargin fifiko a mukaman siyasa.
Da ya juya kan shugabancin jam'iyyar ta kasa kuwa, matashin yace wajibin APC ne ta martaba yarjejeniyar da tayi na baiwa yankin arewa jagorancin jam'iyya domin a rabon mukamai muna baya, ko hukumomin gwamnatin tarayya da aka kafa dan cigaban yankunan jahohin kasar nan, yankin mu na arewa ta tsakiya anai muna abinda aka ga dama, misali hukumar raya cigaban yankin arewa wadanda aka zabo ba a ba su wata damar taka rawar gani ba, illa an ajiye su a matsayin mambobi.
Akwai korafe korafe da dama a zukatan yayan jam'iyya kuma sun yi shiru koda sun yi korafi ba a sauraren su. Da gudunmawar kuri'un mu aka kafa jam'iyyar nan, amma muna kallo wadanda suka hauro ta katanga ke cin moriyarta.
Yanzu dai lokaci bai kure ba, kuma idan ana bukatar gyara za a iya gyarawa muna da shekaru biyu a gaba, yan majalisun da ake tarairaya da yawan su ko mazabunsu ba zasu iya kawo ba.
Ya zama wajibi talakawan nan da ake ganin ba komai ba a koma a rarrashe su.
No comments