A wani mataki na sauƙaƙa samun damar yin biza na Birtaniya ga matafiya daga Arewacin Nijeriya, kamfanin VFS Global tare da haɗin...
A wani mataki na sauƙaƙa samun damar yin biza na Birtaniya ga matafiya daga Arewacin Nijeriya, kamfanin VFS Global tare da haɗin gwiwar Hukumar Biza da Shige da Fice ta Birtaniya (UKVI) sun kaddamar da sabuwar Cibiyar Aikace-aikacen biza ta Musamman a Kano.
An buÉ—e cibiyar ne a Bristol Palace Hotel, lamba 54–56 titin Guda Abdullahi, inda za ta bai wa mazauna Kano da sauran yankunan Arewa damar gabatar da buÆ™atun biza da yin rijista cikin sauÆ™i, musamman kafin lokacin tafiye-tafiyen bazara da ke tunkarowa.
Hajiya Gill Lever, wadda ke matsayin Chargée d’Affaires a ofishin jakadancin Birtaniya da ke Abuja, ta bayyana jin daÉ—inta game da faÉ—aÉ—a ayyukan bada biza a Nijeriya.
“Ina farin cikin tabbatar da ci gaba da faÉ—aÉ—a ayyukan bada biza na Birtaniya a faÉ—in Nijeriya, da kaddamar da sabuwar Cibiyar Aikace-aikace ta Musamman ta VFS a Kano,” in ji ta. “Kano da sauran Arewacin Nijeriya na da matuÆ™ar muhimmanci a dangantakar Birtaniya da Nijeriya. Sabuwar cibiyar za ta taimaka wajen sauÆ™aÆ™a wa mutane samun ingantaccen sabis na biza a kusa da inda suke.”
Ta kuma bayyana cewa Nijeriya na daga cikin ƙasashen da ke da yawan masu ziyartar Birtaniya daga nahiyar Afirka, inda take cikin ƙasashe huɗu mafi yawan masu nema, kuma tana da kusan kashi 6 cikin 100 na adadin aikace-aikacen biza a duniya.
Wannan cibiyar da aka buɗe a Kano ita ce ta uku da VFS Global ta kaddamar a cikin 'yan watannin baya a Nijeriya, bayan buɗe makamantansu a Enugu da Port Harcourt. Cibiyoyin na ƙara wa waɗanda ke Abuja da Legas (Ikeja da Victoria Island), waɗanda ke aiki tun daga Nuwamba 2024.
Mista Alok Singhal, shugaban yankin hamadar nahiyar Afirka na VFS Global, ya jaddada aniyar kamfanin na kawo sauƙi ga abokan cinikinsu.
"Muna farin ciki da Æ™ara yawan wuraren da za a iya samun sabis na biza cikin sauÆ™i ga ‘yan Nijeriya, musamman da buÉ—e sabuwar cibiyar mu ta Musamman a Kano,” in ji shi. “Yayin da buÆ™atar tafiya zuwa Birtaniya ke Æ™aruwa, burinmu shi ne mu samar da irin ingantaccen sabis, sauÆ™i da jin daÉ—i da muke bayarwa a Abuja da Legas a nan Kano.”
Sabuwar cibiyar da ke Kano na bayar da sabis na musamman da suka haɗa da taimako wajen lodin takardu, sanarwa kai-tsaye kan matsayin aikace-aikace, da isar da takardu ta hanyar sakonni. Haka kuma, abokan ciniki za su iya amfani da sabis ɗin "Ajiye Fasfo ɗina Bayan sa hannu", wanda ke ba su damar ci gaba da amfani da fasfo ɗinsu bayan rijistar, sannan su miƙa shi daga baya idan an yanke hukunci.
Kamfanin VFS Global wanda ke aiki da 'UK Visas and Immigration' tun shekarar 2003, ya soma bayar da sabis a ƙasashe 58. A shekarar 2023, an sake ba su kwangilar bayar da sabis a ƙasashe 142, alamar yarda da ƙwarewarsu a fannin.
Ana iya yin rajista don ziyartar sabon Cibiyar Aikace-aikacen biza ta Musamman da ke Kano ta hanyar dandalin yanar gizo na hukuma:
👉 https://visa.vfsglobal.com/nga/en/gbr/
Ga mazauna Kano da sauran yankunan Arewacin Nijeriya, wannan sabuwar cibiyar na nufin Æ™arin sauÆ™i, jin daÉ—i da saurin aiki – wanda zai Æ™arfafa dangantaka tsakanin Nijeriya da Birtaniya a fannonin kasuwanci, yawon buÉ—e ido, ilimi da musayar al’adu.
No comments