Daga El-Bash Abdullahi Tabbas Mallam Abdulaziz Abdulaziz ya cancanci dukkan wani yabo da jinjina daga al’umma duba da ƙoƙari da jajircewars...
Daga El-Bash Abdullahi
Tabbas Mallam Abdulaziz Abdulaziz ya cancanci dukkan wani yabo da jinjina daga al’umma duba da ƙoƙari da jajircewarsa wajen ganin ya taimaki mutane ba tare da duba bambancin ra’ayi, manufa, ko wani saɓani na siyasa ko wata aƙida ba. Lallai yabon gwani ya zama dole.
A tsarinmu idan muna tare da kai za mu haska maka ka taimaki al’umma ka yi musu hidima, ko ba komai akwai mutanen da Allah Ya ƙaddara masu arziƙi ne wata rana za su iya tunawa su dawo su taimake ka a lokacin da kake buƙatar taimakonsu.
Duk da cewa a tsari irin na Malam Abdulaziz babu wannan, shi yana taimakon mutane ne kai tsaye da kykkyawar niyya, kuma ba dole sai kana ra’ayinsa ba, har ƴan jam’iyyar adawa ma taimaka musu yake yi, shi isa za ku ji ana yabonsa ta kowane ɓangare.
Akwai ƴan siyasar da babu abin da ke shiga tsakaninsu da yaransu ko mutane sai na DATA ko ɗan abin da bai taka kara ya karya ba wanda bai fi su cinye shi a yau ba. Saboda suna ƙyashin su taimakawa wani ya fi su. In dai za ka taimaki mutum kawai ka taimake shi don Allah, kar ka taɓa tunanin za ka yi nasara in ba ka taimaki mutane ba.
Ko shugaban ƙasa Tinubu da ake ganin ya zama gagara-badau mutane ya taimaka, ya gina jama’ar da wasu ma ya manta da ya taimake su, amma suna tsaye tare da shi.
Yanzu kan matasa ya waye duk matsayinka in ba za ka taimake su ba to fa ba za su bi ka ba, wanda ko yake taimakon al’ummar za ka ga kowane lokaci jama’a na tare da shi kamar dai Mallam Abdulaziz Abdulaziz ɗin.
A falsafar Romawa sun ce "murya jama'a ita ce muryar Ubangiji", muna fatan yadda al’umma suka yarda da shi suke yaba wa da ƙoƙarinsa, Allah Shi ma Ya yarda da shi ya karɓi wannan ƙoƙari nasa a nan Duniya da gobe ƙiyama.
No comments