Shugaban kamfanin SKY Alhaji Kabiru Sani Kwangila Yakasai (SKY) ya ce ba zai iya rike mukamin Uban Gammayya kungiyoyin yan kasuwa na jihar K...
Shugaban kamfanin SKY Alhaji Kabiru Sani Kwangila Yakasai (SKY) ya ce ba zai iya rike mukamin Uban Gammayya kungiyoyin yan kasuwa na jihar Kano ba, wanda kungiyar ta nada shi makon da ya gabata bayan rasuwar Alhaji Aminu Dantata.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da SKY ya sanyawa hannu da kansa kuma Mai magana da yawunsa Kamal Yakubu Ali ya aikewa manema labarai.
Ya ce mukamin da su ka ba shi Babban Mukami ne da ba zai iya dauka ba, don haka ya yanke shawarar sauka daga mukamin kwanaki uku bayan nada shi.
Yakasai ya ce “Jama’a muna kara godiya da duk ni’imar da Allah ya yi mana da kauna da ake nuna mana dare da rana da girmamawa da ake mana.
“Ina bada hakuri da fatan alheri ga gamaryar kungiyoyi yan kasuwar jihar Kano bisa nadi da suka yimun na shugabancinsu a matsayin UBA NA KUNGIYA da su yi hakuri a kan wannan matsayin ya yi min nauyi bazan IYABA. Amma ina tare da su a duk al’amuransu musamman inda ake bukatar gudunmawata.
“Allahumma Salli Ala Sayyidanan Muhammad wa ala alihi” Ni Alhaji Kabiru Sani Kwangila Yakasai (SKY) ina mika ta aziyyar ga al’ummar Nigeria gaba daya bisa rasuwar babanmu Alhaji Aminu Alhassan Dantata da sauran mutanen da muka rasa baki daya mace da namiji, Allah ya gafartamusu amin.
No comments