Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Ayyukan Tinubu da Gwamna Abdullahi Sule za su ba su damar lashe zaben 2027 - Al'ummar Nasarawa ta Arewa

Daga Zubairu Lawal  Shugabannin jam'iyyar APC da masu ruwa da tsaki a yankin Nasarawa ta Arewa sun bayyana amincewarsu da Gwamnatin Shug...


Daga Zubairu Lawal 

Shugabannin jam'iyyar APC da masu ruwa da tsaki a yankin Nasarawa ta Arewa sun bayyana amincewarsu da Gwamnatin Shugaba Bola Ahmad Tinubu da Gwamna Abdullahi Sule a matsayin Gwamnatin da ta kawo cigaba.  

Sun kuma tabbatar da basu kuri'a a zaben 2027 suna goyon bayan takarar Tinubi na sake maimata kujerar Shugabancin kasa a karo na biyu da Gwamna Abdullahi Sule a matsayin kujerar Majalisar Dattawa a yankin Nasarawa ta Arewa. 

Shugabannin Jami'iyyar APC da suka fito daga Kananan hukumomin Akwanga Nasarawan Eggon da Wamba, sunce sun gamsu da mulkin Gwamna Abdullahi Sule da ya gudanar a jihar Nasarawa, saboda ya kawo zaman lafiya mai dorewa da hadin kan al'umman jihar. Ya kuma yi ayyuka a jihar Nasarawa da yankin Nasarawa ta Arewa. 

Da yake karanta jawabi tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Nasarawa, mista Timothy Anjide, yace wannan kirane da gamayyar al'umman yankin Nasarawa ta Arewa sukayi bayan haÉ—in gwiwa inda masu ruwa da tsaki na APC suka sha alwashin ci gaba da goyon bayan manufofi Gwamnatin Abdullahi Sule da shirye-shiryen da ke inganta rayuwar al’ummar yankin da jihar baki daya. 

Ya kuma bayyana cikakken goyon bayansu ga burin Shugaba Bola Tinubu na sake tsayawa takara a 2027, masu ruwa da tsakin sun yabawa Shugaban kasa bisa yadda ya naÉ—a ’ya’ya maza da mata daga yankin Nasarawa ta Arewa a manyan mukamai na hukumomin tarayya, kwamitoci da cibiyoyi.

Da yake zantawa da manema labarai bayan kammala taron masu ruwa da tsaki na APC a yankin Nasarawa ta Arewa, Shugaban Ƙaramar Hukumar Akwanga kuma Shugaban Ƙungiyar Shugabannin Kananan Hukumomi ta jihar Nasarawa (ALGON) , Hon. Safiyanu Isa Andaha ya ce taron an shirya shi ne domin tattauna hanyoyin cigaba da Æ™arfafa jam’iyyar da mambobinta a yankin.

Ya Æ™ara da cewa: “An cimma matsaya baki É—aya cewa Mai Girma Gwamna Abdullahi Sule ya kamata ya tsaya takarar Sanata a zaÉ“en 2027. Ina da tabbacin cewa gwamnanmu, wanda ya gaji tsarin dimokuraÉ—iyya, zai saurari muryar jama’arsa ya amsa kiranmu.”

“Baya ga amincewar da aka yi wa Shugaba Bola Tinubu da Gwamna Sule don zaÉ“en 2027, wani babban dalilin taron shi ne Æ™arfafa haÉ—in kan jam’iyya. Mun yi magana da kanmu cewa domin ci gaban jam’iyyar, dole ne mu watsar da duk wata gaba ko sabani mu haÉ—a kai mu yi aiki tare a matsayin al’umma.”

No comments