Daga Awwal Umar Kontagora Kungiyar leburori masu haƙar ma'adanin ƙasa (Nigeria Union Of Mine Workers) ta shirya kaddamar da ...
Daga Awwal Umar Kontagora
Kungiyar leburori masu haƙar ma'adanin ƙasa (Nigeria Union Of Mine Workers) ta shirya kaddamar da shugabannin kungiyar na karamar hukumar Magama.
Tunda farko a bayaninsa, bayan karban takardun amincewa da shugabannin, shugaban kungiyar a jihar Neja, Kwamred Musa Adamu Nasko, yace bisa doka bayan shugabancin tarayya akwai na jahohi, bayan su kuma akwai na kananan hukumomi, yanzu ayyukan da muka sanya a gaba, kamar yadda doka ta tsara bisa yunkurin gwamnatin jiha, karkashin gwamnatin Dakta Umar Mohammed Bago ta zo da tsare tsaren inganta ayyukan mu wajibi ne mu tabbatar kamar yadda aka samar da shugabancin jiha mun samar da shugabancin dukkanin kananan hukumomi, wanda mun rantsar da kananan hukumomi da dama.
Bisa lura da tsare tsaren kungiyar a karamar hukumar Magama, bayan sun bi ka'idodin kungiya za mu rantsar da su nan bada jimawa dan soma ayyukan su bisa doka.
Saboda ina shawartar duk wani dan ma'adani da ke son cin gajiyar sana'arsa ya tabbatar ya kiyaye doka kamar yadda kudin dokokin kasa ya tanada, kuma ya tabbatar ya kiyaye dokokin da gwamnatin jiha ta tsara, hakan ba zai yiwu ba sai ta hanyar kungiya.
Da yake tsokaci, mai bincike na kungiyar, Alhaji Yahaya Anfani, yace bisa bincikensa ya gamsu da hanyoyin da aka bi wajen fitar da shugabancin karamar hukumar Magama.
Kan haka ya shawarci uwar kungiya ta jiha, da ta gaggauta rantsar da su kamar yadda doka ta tsara, domin duk wani ka'ida sun cika su kuma dukkaninsu sun cancanci rike kujerun da aka ba su.
" Ina jawo hankalin duk wani dan ma'adani ya baiwa wadannan shugabanin goyon baya, domin za su yi aiki ka'in da na'in da tsare mutuncin duk wani dan ma'adani a karamar hukumar Magama".
Hajiya Maryam Ibrahim, wadda itace zavta dare kujerar shugabar mata, tace maganar harkar ma'adani a kasar Magama ba a bar mata a baya ba. Domin mun lura maza sun yi mana zarra a wajen neman abinci.
Kadancewar mu jajirtattu, mun rungumi wannan harkar a kasar Magama, wanda a yau kafada da kafada mu ke yi da maza wajen harkar ma'adani.
Zan tabbatar duk wani abinda ya shafi ka'idodin hakar ma'adani kamar yadda doka ta tsara mun bi shi. Mun yabawa gwamnatin jiha bisa kishi da kokarinta na inganta wannan sana'ar ta mu.
Kwamred Usman Bashi Garafuni, wanda shi dan takarar kujerar shugabancin kungiyar tilo da ya nuna sha'awarsa ga neman kujerar, ya nemi yayan kungiyar da su tabbatar sun jefa mai kuri'unsu ko sun amince da shi dan samun shugabanci na adalci.
Ya cigaba da cewar hadin kai, da goyon bayan su shi zai karfafa guiwarsa wajen jajircewa dan ganin an yi abinda ya dace.
Idan kana maganar aikin ma'adani ne a jihar Neja, idan Magama ba ta zo ta farko ba kuma ba za ta zama ta karshe ba, dan muna sahun gaba wajen samarwa gwamnati kudaden shiga da samar da gurabun ayyukan yi ga matasa.
Garafuni, ya shawarci jami'an tsaro da su hada kai da su wajen ganin kowani dan ma'adani ya bi dokokin gwamnati, da kuma tabbatar da kowani dan ma'adani yayi rajista da gwamnati a kungiyan ce dan samun damar tsaftace aikin kamar yadda gwamnati ta umurta.
No comments