Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Ƙungiyar Matasan Fulani sun sha alwashin marawa gwamna Umar Bago a zaɓe mai zuwa

Daga Awwal Umar Kontagora Kungiyar matasan Fulani mai suna 'Fulani Youth Bago Again 2027' ta sha alwashin marawa gwamna....

Daga Awwal Umar Kontagora

Kungiyar matasan Fulani mai suna 'Fulani Youth Bago Again 2027' ta sha alwashin marawa gwamna.Umaru Bago na jihar Neja dan ganin ya dawo kam kujerar gwamnatin Neja karo na biyu a zaben 2027 mai zuwa. Kodinetan kungiyar, Amb. Mujahid Adam ne ya bayyana hakan lokacin da shugabancin kungiyar ta kai ziyarar nuna goyon baya ga manufofin gwamnatin Neja na inganta rayuwar manoma da makiyaya ga kwamishinan ma'aikatar kula da jin dadin makiyaya da manoma, Hon. Umar Sanda Rebe ( Janwuron Minna).

Tunda farko a bayanin shugaban ya yabawa jajircewar kwamishinan bisa lura da ayyukan da ya sanya a gaba, ganin ma'aikatar irinta ce ta farko da gwamnati ta kirkira dan inganta rayuwar makiyaya da manoma tare da janyo su a jika dan sauraren bukatunsu ta yadda zasu samu damar cin moriyar mulkin dimukuradiyya. 

Amb. Mujahid, ya cigaba da cewar ba mun kafa wannan kungiyar ba ne dan cin zarafin wasu ko zama kishiya ga wasu ba, mun kafa tafiyar dan bada ta mu gudunmawa ta yadda kowani makiyayi da manomi zasu samu damar matsuwa kusa da gwamnati.

Muna da shirye shirye da dama, da suka shafi koyar da al'ummar Fulani sana'o'in hannu, bayan kiwo da karfafa su wajen mayar da hankali kan neman ilimin zamani da na addini, wanda muna kyautata zaton zai taimaka wajen ceto yayan Fulani da makiyaya daga jahilcin da ya jefa mafi yawan matasan mu a wannan mummunar yanayin da suka tsinci kan su, na aikata ayyukan da ba su dace ba.

Idan dukkanin kungiyoyi suka fito muka hada hannu kuma muka yi aiki tare muna da kwarin guiwar gwamnatin Dakta Umaru Bago za ta cin ma nasarar da take nema, tare da shan alwashin cigaba da wayar da kan makiyaya muhimmancin mnufofin gwamnatin nan da muka dade muna fatar ganinsa a jihar nan.

Da yake tsokaci ga shugabannin kungiyar, kwamishina a ma'aikatar, Hon. Umar Sanda Rebe, yace sake da wasiyar Shehu Usmanu Danfodio ne ya janyo halin da ake ciki yau, yace Danfadio yace wa al'ummar Fulani ku nemi ilimi, ku yi noma da kiwo, amma sai muka rungumi kiwo da noma mu ka yi watsi da batun ilimi, wanda ya janyo da yawan yayan mu suka watsar da akidar mu na fullako, wato kunya, biyayya da tsaurin kai.

Zuwan gwamna Umaru Bago ya sha alwashin kafa ma'aikatar makiyaya da manoma kuma ya cika wannan alkawalin. Yau a kankanin lokaci an samu nasarori masu yawa, babban abinda muke nema hadin kai, dole sai da hadin kai da kiyaye dokokin kasa ne gwamnati za ta samu kwarin guiwar yin anfani da kuri'un mu wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyan ta.

Daga cikin ka'idodin da muka cin ma kafin samun wannan matsayin, gwamna yace dole sai cikakken dan jiha, bafullatani jajirtacce ne za a baiwa wannan matsayin, kuma mun cika wannan ka'idar. Bayan kujerar kwamishina da muke da shi, muna da babban darakta, kuma muna da mukaman kodineta guda biyar, yanzu haka makiyaya sittin da takwas suka samu gurbin ayyukan gwamnatin jiha, bayan tallafin karatu da yayan mu suka samu shekaru da kafuwar gwamnati.

Dan haka gwamna bai ga kuri'a ba a zaben 2023 sai zabe mai zuwa domin yake bin ba shi yanzu. Muna cikakken kudin bayanai na adadin fulanin jihar nan da adadin dabbobin da muke da su na kusan kananan hukumomi da dama, wanda muna da kudurin tattara sauran bayanai kafin nan da wani lokaci kalilan.

Gwargwado mun san matsalolin Fulani makiyaya, nasarar da muka samu yafi korafe korafen da ke gaban mu yawa.

Ku zo mu hada kai, kowani basarake ya tabbatar ya karfafa guiwar al'ummarsa muhimmancin neman ilimi domin gwamnati a shirye take wajen sauke wannan nauyin. Ba mu cirewa kowa hula ba, ku zo mu hada kai mu yi aikin nan tare, muna burin nan gaba idan an ajiye abu gaban bafillatani har ya rube ba mai taba saboda tsantsenin mu. Yanzu da kafa wannan ma'aikatar mukamai dubu takwas muka samu.

A na sa jawabin, kodinetan Bago Ruga Ruga ta jihar Neja, Alhaji Hassan Usman Shiroro ( Wakilin Fulanin Minna), ya yabawa matasan wajen yunkurin kafa wannan tafiyar, sai dai ya jawo hankalin matasan da su zo a hada a gudu tare a tsira tare domin duk wani gatan da muke nema a gwamnatance gwamnatin Umaru Bago tayi mana.

Kwamared Sulaiman Ruga, shi ne babban sakataren sabuwar kungiyar, ya bayyana cewar mun fito dan nuna goyon baya da bada gudunmawar ga gwamnatin jiha dan nasarar da take nema. Tun kafuwar kungiyar mun shiga lungu da sako dan isar da sakon manufofin gwamnatin jiha kan haka muke neman goyon bayan ma'aikatar dan cigaba da wannan aikin da muka sanya a gaba.

No comments