Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamnatin Zamfara Ta Rattaba Hannu Kan Wata Yarjejeniyar Sabunta Biranen Jihar

  Gwamnatin jihar Zamfara ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya ta fara aikin sabunta biranen kashi na daya a babban birnin jihar. Kashi na ...

 


Gwamnatin jihar Zamfara ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya ta fara aikin sabunta biranen kashi na daya a babban birnin jihar.

Kashi na daya na aikin na babban birnin shi ne aikin hanyar da ta hada gidan gwamnati da titin Bello Bara’u, titin Tankin Ruwa, da tsohuwar hanyar kasuwa, da shataletalen ofishin ‘yan sanda da dai sauransu.

Kakakin Gwamnan, Sulaiman Bala Idris, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, ya ce an rattaba hannu kan yarjejeniyar kwangilar ne a zauren majalisar na gidan gwamnati.

Ya kara da cewa, samar da ababen more rayuwa wani bangare ne na kudirin Gwamnatin jihar domin sabunta birane da nufin samar da yanayi mai kyau ga ‘yan kasuwa domin su bunkasa da samun saukin rayuwa.

Sanarwar ta kara da cewa: “Gwamnatin jihar Zamfara ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya da wani katafaren kamfanin gine-gine, Ronchess Nigeria Limited domin fara shirin sabunta birane a jihar.

“Gwamna Lawal ya jaddada kudirin Gwamnatinsa na ganin an gyara kayayyakin ababen more rayuwa ta hanyar sake gina sabbi da kuma gyara tsofaffin da suka lalace wanda za a fara daga babban birnin jihar.

“shirin sabunta biranen zai fara ne da titunan babban birnin ta Gusau, wanda wannan shi ne zai zama mafarin samar da ababen more rayuwa da za su mamaye dukkan kananan hukumomin jihar.

“Rattaba hannu kan yarjejeniyar kwangilar yana nuna cewa Gwamnatin jihar Zamfara ta fara wani aiki da zai sauya labari zuwa mai kyau.

“Gwamnati za ta samu nasarori da dama tare da hadin kan mutanen kirki na jihar Zamfara. Sabunta birni yana É—aya daga cikin dabarun da za a yi amfani da su domin aiwatar da aikin ceto."

Da yake mayar da bayani a madadin kamfanin gine-ginen, babban daraktan kamfanin na Ronchess, Samson David ya bayyana cewa suna son su maida birnin Gusau kamar yadda suka yi a jihar Kaduna. Ya kuma yabawa gwamnatin jihar Zamfara bisa zabarsu a matsayin wadanda suka cancanta aka ba su wannan kwangilar tare da bada tabbacin cewa za su gudanar da ayyukan yadda yakamata.

No comments