Daga Hassan Ibrahim A ranar Asabar ɗin da ta gabata ne, Mai Martaba Sarkin Zazzau Malam Ahmad Nuhu Bamalli ya amince da naɗin Arc. Zakari Mo...
Daga Hassan Ibrahim
A ranar Asabar ɗin da ta gabata ne, Mai Martaba Sarkin Zazzau Malam Ahmad Nuhu Bamalli ya amince da naɗin Arc. Zakari Mohammed Saleh (Annur) a matsayin sabon Sarkin Arab wanda ɗan Barhin Zazzau, Hakimin Sabon Gari, Alhaji Ahmed Bashir Aminu ya tabbatar da naɗin nasa, wanda ya gudana a ofishin Hakimin dake ƙaramar hukumar Sabon Garin Zariya ta jihar Kaduna.
Ƴan uwa da abokanan arziƙi, na nesa da na kusa sun zo don taya shi murna bisa samun wannan sarauta.
A zantawarsa da manema labarai, Sarki Arab ya godewa Allah (SWT) da ya nuna mishi wannan rana don shaida wannan naɗi da aka yi masa wanda a cewarsa, wannan babban rana ce a gare shi ta farin ciki a ɗaukacin rayuwarsa baki ɗaya.
"Zan iya cewa kusan ni ne na uku, wanda ya riƙe wannan sarauta, na farko shi ne Kakanmu Alhaji Hussaini, daga shi sai Kawunmu, Alhaji Musa Hussaini Sarki Arab shi ne ya rasu kafin nan aka bani, ina fatan Allah ya jiƙansu da Rahama baki ɗaya." In ji shi.
Ya kuma yi godiya ga ɗimbin al'umma da suka halarci nadin nasa tare da musu fatan alkhairi da kuma fatan Allah ya sa kowa ya koma gidansa lafiya.
Kazalika, ya miƙa cikakken godiya ga mai Martaba Sarkin Zazzau Malam Ahmad Nuhu Bamalli bisa irin wannan karamci da aka yi masa.
Taƙaitaccen tarihin sabon Sarki Arab
Zakari Mohammed Saleh (Annur) mazaunin ƙaramar hukumar Sabon Garin Zariya ta jihar Kaduna, ya yi karatun Nursery, Firamare da Sakandire a makarantar Therbow School dake GRA, Zariya.
Daga nan ya tafi makarantar karatun share fagen shiga jami'a wato (SBRS) dake Funtua, inda ya sami shekara ɗaya, wanda ya bashi damar shiga jami'ar Ahmadu Bello Zariya inda ya sami shekara huɗu a fannin gine-gine wato (Architecture).
Kammala karatunsa ke da wuya,ya tafi ƙasar Ingila inda ya sami digirin sa wato (Masters) a Construction Management, inda ya dawo ƙasa Nijeriya ya yi bautar ƙasarsa a ƙaramar hukumar Boko ta jihar Binuwe.
Daga bisani ya sami aiki a jihar Katsina a matsayin SSA Protocol na matan gwamnar jihar Katsina
Daga nan ya ci gaba da karatunsa zuwa ƙasar Turkiya inda ya yi digirinsa na biyu a fannin gine-gine (Architecture).
Bayan dawowarsa ƙasa Nijeriya a shekara ta 2015 ya sami aiki da jami'ar Jihar Kaduna wato (Kaduna State University) a matsayin malami a sashin koyar da fasahar gine-gine (Architecture) har zuwa tsawon wannan lokaci.
No comments