Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Tinubu ya naɗa ƙarin tsoffin gwamnoni biyar ministoci

Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Godswill Akpabio ya bayyana ƙarin sunayen mutum 19 da Shugaba Bola Tinubu ya aika musu domin naɗa su mi...


Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Godswill Akpabio ya bayyana ƙarin sunayen mutum 19 da Shugaba Bola Tinubu ya aika musu domin naɗa su ministoci.

Cikin jerin har da tsofaffin gwamnoni biyar da suka haɗa da Bello Matawalle na Zamfara, da Atiku Bagudu na Kebbi, da Gboyega Oyetola na Osun.

Sauran tsofaffin gwamnonin su ne Ibrahim Geidam na Yobe, da Simon Lalong na Jihar Filato.

Shugaban Ma'aikatan Fadar Shugaban Ƙasa Femi Gbajabiamila ne ya kai wa Majalisa sunayen a madadin shugaban ƙasa bayan 28 da ya bayar tun farko.

No comments