Mai magana da yawun rundunar sojin Najeriya, Birgediya JanarTukur Gusau, ya ce manyan hafsoshin tsaronƙungiyar Ecowas za su samar da mafit...
Mai magana da yawun rundunar sojin Najeriya, Birgediya JanarTukur Gusau, ya ce manyan hafsoshin tsaronƙungiyar Ecowas za su samar da mafita idan dukkan hanyoyin da aka bi a siyasance ba su yi tasiri ba bayan juyin mulki a Nijar.
"Matakin soji zai zama na ƙarshe da za a ɗauka," kamar yadda ya shaida wa BBC.
Manyan hafsoshin tsaron ƙungiyar ta raya tattalin arzikin ƙasashen Afirka ta Yamma na tattaunawa a Abuja daga yau Laraba zuwa Juma'a domin tattaunawa kan hanyoyin da za a bi wajen shawo kan sojojin da suka yi juyin mulkin, inda aka hamɓarrar da gwamnatin Shugaba Mohamed Bazoum a makon da ya gabata.
Manyan hafsoshin tsaron Ghana, da Najeriya, da Benin, da Togo, da Saliyo, da Laberiya, da Gambiya, da Cote D’Ivoire, da Cape Verde ne ke halartar taron.
Sai dai takwarorinsu na Mali, da Nijar, da Guinea Bissau, da Burkina Faso, da Guinea ba su halarta ba sakamakon dakatar da su da Ecowas ta yi daga ƙungiyar saboda juyin mulkin da suka jagoranta a ƙasashensu.
Manyan hafsoshin tsaron za su gabatar da matakin da suka cimma ga shugaban ƙungiyar Bola Tinubu a ranar Juma'a.
Daga nan ne shugaban ƙungiyar zai yanke shawara kan mataki na gaba da za a ɗauka kan sojojin ƙarƙashin jagorancin Janar Abdourahmane Tchiani, wanda ya ayyana kan sa a matsayin shugaban Nijar.
No comments