Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

'Yan ƙwadago sun gana da Tinubu bayan gama zanga-zanga

  Shugabannin ƙungiyar ƙwadago a Najeriya sun kammala ganawa da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu a fadarsa da ke Abuja. An yi ganawar 'yan sa...

 


Shugabannin ƙungiyar ƙwadago a Najeriya sun kammala ganawa da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu a fadarsa da ke Abuja.

An yi ganawar 'yan sa'o'i bayan mambobin ƙungiyar sun yi zanga-zangar ƙasa baki ɗaya don yin tir da cire tallafin man fetur.

Yayin zanga-zangar, 'yan ƙwadagon sun shiga zauren Majalisar Dattawan Najeriya, inda Mai Tsawatarwa na Majalisa Sanata Ali Ndume ya tarɓe su.

Zuwa yanzu ba a bayyana abin da ɓangarorin suka tattauna ba, da kuma ko sun cimma wata matsaya.

No comments