Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya shaida wa majalisar dokokin Najeriya matsayar da ƙungiyar Ecowas ta cimma kan ɗaukar matakin soji a...
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya shaida wa majalisar dokokin Najeriya matsayar da ƙungiyar Ecowas ta cimma kan ɗaukar matakin soji a kan Nijar da kuma sauran takunkuman da aka ɗauka na ladabtar da sojojin da suka yi juyin mulki.
Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Godswill Akpabio ya sanar da saƙon shugaban ƙasar inda ya karanto kai tsaye daga wasikar shugaba Tinubun.
Wasikar na cewa “Bayan abin takaicin da ya faru a Nijar inda aka hamÉ“arar da shugaban Æ™asa, Ecowas a Æ™arÆ™ashin jagorancina ta yi Allah-wadai da juyin mulkin kuma ta amince da É—aukar matakan dawo da Nijar kan turbar dimokuraÉ—iyya. A wani mataki na dawo da zaman lafiya a Æ™asar Ecowas ta fitar da matsaya.
“Za a rufe duk iyakokin Nijar da Æ™asashenmu da kuma sanya ido don tabbatar da cewa an yi biyayya ga matakin.
“Yanke wutar lantarkin da ake kaiwa Nijar da neman goyon bayan Æ™asashen duniya wajen aiwatar da matsayar Æ™ungiyar Ecowas da kuma datse sufurin jirgin sama daga cikin Nijar da ma wanda zai shiga Æ™asar.
“Rufe hanyoyin shigar da kaya Nijar daga Legas da kuma wayar da kan Æ´an Najeriya musamman a kafafen sada zumunta game da shirin É—aukar matakin soji a kan sojojin Nijar É—in.''
No comments