Sanatoci ba su yi tambayoyi ga Bello Matawalle ba a wajen tantance shi a matsayin minista daga jihar Zamfara. Mataimakin Shugaban Majalisa...
Sanatoci ba su yi tambayoyi ga Bello Matawalle ba a wajen tantance shi a matsayin minista daga jihar Zamfara.
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattijai, Barau Jibril ya ce Matawalle mutum ne mai ƙima saboda haka ya bayar da shawarar ya yi gaisuwa ya wuce.
A lokacin da Matawalle ya kammala bayani kan rayuwarsa, Sanata Abdula'aziz Yari ya yaba tare da buƙatar majalisa ta amince da tsohon gwamnan na Zamfara ba tare da yi masa wasu tambayoyi ba.
Sauran waɗanda suka yaba wa Matawalle sun haɗa da Kawu Sumaila, da Abdula-Azeez Ƴar'adua da kuma Sanata Ali Ndume.
Matawalle tsohon gwamnan jihar Zamfara ne da ya sha kaye wajen jam'iyar adawa ta PDP.
No comments