Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Ƙungiyar Taimakon Juna Da Marayu Ta Yi Taron Taimakawa Marayu A Garin Bomo A Karo Na Uku

Daga Idris Umar Zariya Kungiyar taimakon juna da marayu ta gabatar da taron bayar da tallafi ga marayu a garin Bomo a ƙaramar hu...

Daga Idris Umar Zariya

Kungiyar taimakon juna da marayu ta gabatar da taron bayar da tallafi ga marayu a garin Bomo a ƙaramar hukumar Sabon Gari ta jihar Kaduna.

Taron ya sami halartar manyan baƙi da suka haɗa da limamai da Sarakuna da manyan ma'aikata da sauran mutanen garin Bomo da kewaye.

Mai Martaba Sarkin ƙasar Bomo Alhaji Muktar Salisu shi ne ya zama babban bako a wajen taron.

Yayin da yake jawabi a wajan taron sarkin na Bomo ya nuna jin dadinsa bisa kokarin da kungiyar takeyi na taimakon juna tare da tallafawa marayu a irin wannan lokacin ya ce, "Hakan abin koyi ne ga musulmi baki ɗaya" 

Karshe Sarkin ya dankawa kowanne maraya sadaka tare da yin masu addu'ar gamawa lafiya. 

Shima Shugaban ƙungiyar Alhaji Ishaq Ayuba a yayin da yake jawabisa ya nuna jin dadinsa bisa yadda ya ga an ba su goyan baya.

Ya ce bai taɓa zaton taron zai yi armashi kamar yadda ya yi ba amma sai gashi lamarin ya wuce yadda suke zata.

Daga karshe ya ce kungiyar ta su na gaiyatar dukkan mai son tafiya a cikinta kuma yace, kofarsu a bude take ga duk mai son bayar da taimakonsa ga marayu ko wasu mutane.

Shugaban ya baiwa marayun hakuri bisa yadda al'amura suka canza yace, da sannu komai zai warware.

Ƙarshe shugaban ya yi godiya ga Sarkin na Bomo bisa sadaka daya baiwa marayun kuma yayi godiya ga yayan kungiyar bisa jajircewansu akan taimakon juna da taimakawa marayu.

Binciken da wakilinmu ya gudanar ya tabbatar da cewa ƙungiyar ta shekara 3 cur tana gudanar da irin wannan hidimar ga al'uma musamman marayu da sauran jama'a.

Kuma bincike ya tabbatar da kungiyar tana samun kudin da take bayar da tallafin ne ta hanyar bayar da gudummawa a tsakanin juna.

Kuma bincike ya kara tabbatar da cewa hakuri da dauriya da sadaukarwa shine kashin bayar tafiyar kungiyar.

Kuma yanzu haka kungiyar na samun kalubale na rashin kudi da kayan masarufi wanda suke bayarwa ga marayun da sauran mabukata.

Amma kuma kungiyar na samun nasara wajan samun hadinkan juna da samun fadimtar juna.

Daga cikin manyan bakin da suka Sami zuwa wannan taron akwai Dakta Musa Dalladi Bomo da Hajiya Rukaiyat Shuibu Ubale mai maciji Samaru da sauran mutanen garin Bomo da kewaye

An yi taro lafiya an tashi lafiya.

No comments