Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gyaran Hanyar Kontagora Zuwa Rijau Zai Taimaka Wajen Farfado Da Tattalin Arzikin Yankin - Hamdala

  Daga Awwal Umar Kontagora An bayyana cewar yunkurin gyaran hanyar Kontagora zuwa Rijau da gwamnatin Neja ke yi abu ne da al'ummar yank...

 


Daga Awwal Umar Kontagora

An bayyana cewar yunkurin gyaran hanyar Kontagora zuwa Rijau da gwamnatin Neja ke yi abu ne da al'ummar yankin suka dade suna mafarkinsa, domin sakamakon lalacewar hanyar ya taimaka wajen tabarbarewar lamurra da dama. Wani jigo a jam'iyyar APC tsohon mEmba a hukumar jin dadin alhazai ta jiha, Alhaji Muhammadu Lawal Hamdala ne ya bayyana hakan lokacin da yake zantawa da manema labarai a Minna.

Hamdala, ya ci gaba cewar kusan shekaru ashirin da biyar ke nan da wannan hanyar ke neman kulawa amma ba a samu gwamnatin da ta sanya damba na gyaran hanyar ba sai bayan zuwan gwamnatin Manomi Umaru Mohammed Bago, wanda wannan yunkurin abin mu al'ummar Rijau mu yaba ne.

Da yawan kananan Karkarun da ke yankin sun tarwatse, wanda muna kyautata zaton ko wadanda suka yi ban kwana da zuwa gida saboda yanayin hanyar zasu samu kwarin guiwar dawowa dan cigaba da noma da kasuwanci.

"Ya kamata duk wani mai kishin kasar Rijau, in har da gaske yake mu kawar da bambancin siyasa da ra'ayi dan marawa gwamnatin baya domin alheri ta zo muna da shi kasar Rijau, saboda haka duk wani jigo a kasar Rijau matashi ne ko dattijo da mu hada dan ganin wannan aikin hanyar ya zama gaskiya.

"Ina da kwarin guiwar wannan gwamnatin da gaske take wajen ceto jihar da farfado da tattalin arzikin al'ummar jihar sakamakon kirkiro ayyukan ci gaban kasa da ta sanya a gaba.

"Alherin da wannan aikin zai samar idan an aiwatar da shi akwai samar da gurabun ayyuka ga jama'a, tare da dawo da martabar yankunan karkarun da ke hanyar da zuwa yanzu suke gab da watsewa", ya tabbatar.

Hamdala, ya shawarci al'ummar jihar da su ci gaba da taimakawa gwamnatin Umaru Bago da addu'o'i musamman akan yaki da ta'addanci da yayi silar durkusar da harkar noma da kasuwanci wanda aka san mafi yawan yankunan jihar akan sa.

Hanyar Kontagora zuwa Rijau hanya ce da ta hada karamar hukumar Kontagora, da wani sashen karamar hukumar Mariga zuwa karamar hukumar Rijau da ke iyaka da karamar hukumar Zuru ta jihar Kebbi. Wanda sakamakon lalacewar hanyar da aka yi tun lokacin mulkin mallaka ya daidaita yankunan karkaru da dama da ya baiwa yan ta'adda damar samun mafaka sakamakon hare haren da suke kaiwa al'umma sakamakon rashin hanyar da za a kaiwa al'umma dauki.

Haka hanyar ita ce babbar hanyar da tafi sauki ga matafiya wadanda ke samun saukin shiga yankunan jihar Kebbi da Zamfara, wadda tsawon tafiyar bai wuce minta arba'in da biyar zuwa awa daya ba, amma yanzu ana daukar kimanin awa biyar zuwa shida kafin shiga garin.

Ranar ashirin ga watan Ramadan da ya gabata gwamnan Neja, Manomi Umaru Mohammed Bago ya kaddamar da aikin hanyar duk da cewar mallakin gwamnatin tarayya ne. 

No comments