Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Kotu Ta Ce ‘Yan Sanda Su Biya Diyyar Naira Miliyan 300 Bisa Kashe ‘Yan Shi’a 3 A Zariya

Sufeto Janar na 'yan sandan Nijeriya Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kaduna ta umurci hukumomin ‘yan sanda da su biya zunzurut...

Sufeto Janar na 'yan sandan Nijeriya

Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kaduna ta umurci hukumomin ‘yan sanda da su biya zunzurutun kudi har Naira miliyan 300 ga iyayen ‘yan Shi’a guda uku da ake zargin jami’anta sun kashe a lokacin da suke gudanar da muzahara a shekarar 2022 a Zariya.

Mai shari’a Hawa Buhari, a cikin hukuncin da ta yanke, ta ce “’yancin masu kara an tabbatar da shi a cikin sashe na 33, 38, 39, 40, 42 da 46 na kundin tsarin mulkin 1999 (wanda aka yi wa kwaskwarima); doka ta 2, da doka ta 1, 2, 3, 4 , 11 da 12 na yarjejeniyar Afrika (African Charter) kan ‘yancin dan Adam da al’umma na 2004 shima an tabbatar da shi.”

Alkaliyar kotun ta ce dole ne a biya adadin kudi har Naira miliyan 100 ga kowanne iyayen wadanda aka kashe, inda za a biya jimillar Naira miliyan 300 ke nan a matsayin diyya da kuma barnar da aka aikata, sannan za a biya ribar kashi 10 cikin 100 a duk shekara har sai an biya kudin baki daya.

Mai shari’a Buhari, a hukuncin da ta yanke a ranar 22 ga Afrilu, 2024, inda aka bai wa manema labarai kwafin hukuncin kotun a Abuja, ta hada dukkanin kararrakin guda uku da makusantan wadanda aka kashe guda uku suka shigar gabanta wuri guda.

“Bayan da lauyoyi suka tabbatar da karar ta su tare da gabatar da shaidu, a don haka kotu ta yi la’akari da haka kuma ta ba da umurni kamar haka:

“Shari’a mai lamba: FHC/KD/CS/138/2022, da mai lamba: FHC/KD/CS/140/2022 da kuma mai lamba: FHC/KD/CS/146/2022 an hada su.

“Dole a biya kudi Naira miliyan 100,000,000.00 (Naira Miliyan Dari) ga kowanne iyayen wadanda aka kashe a matsayin diyya da barnar da aka yi gaba daya tare da biyan ribar kashi 10% a duk shekara har sai an biya kudin duka.

“Wadanda aka shigar da kararrakin dole ne za su ba da hakuri a rubuce ga wadanda suka shigar da kara a daya daga cikin jarida ta kasa da ke fitowa a kowacce rana saboda take hakkinsu da aka yi,” in ji ta.

Idan za a iya tunawa cewa mutane uku ne suka shigar da karar wanda ya hada da; Magaji Yusuf, Muhammad Lawal da Aliyu Badamasi, inda suka shigar da kararraki masu lamba: FHC / KH/ KD/ 138/2022, FHC / KH/ KD/ 140/2022 da FHC / KH/ KD/ 146/2022 a gaban kotu.

Sun yi zargin cewa a ranar 8 ga watan Agusta, 2022, jami’an ‘yan sandan Nijeriya suka harbe Jafar Magaji, Aliyu Lawal da Muhsin Badamasi, a lokacin da suke gudanar da ibadarsu ta Muzaharar Ashura a Garin Zariya.

Sun kai karar Sufeto-Janar na ’yan sanda (IGP), Mataimakin Sufeto-Janar na ’yan sanda na shiyya ta 7, Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Kaduna, AC Surajo Fana (Kwamandan yankin Zariya), Ibrahim Zubairu (Jami'in ’Yan sanda (DPO), Kasuwan Mata, Sabon Gari, Zaria Division), da kuma Kasim Muhammad (DPO, Zaria City Division) a matsayin masu amsa kara na 1 zuwa na 6.

Masu karar a cikin karar da suka shigar a ranar 26 ga Satumba, 2022 tare da kuma gabatar da ita a ranar 26 ga Satumba, 2022, ta hannun tawagar lauyoyinsu da suka hada da H.G Magashi, M.D Abubakar da Dr Yusha’u, sun nemi damarmaki guda bakwai.

Sun nemi da a bayyana cewa harbe-harbe da kashe Jafar Magaji, Aliyu Lawal da Muhsin Badamasi a ranar da aka bayyana sun gudanar da muzaharar su ta addini ya sabawa doka, ya kuma sabawa tsarin mulkin kasa, sannan ya kuma tauye hakkinsu na rayuwa kamar yadda sashe na 33 na kundin tsarin mulkin 1999 da kuma doka ta 4 na YarjejeniyarAfirka kan dokar hakkokin dan Adam da al’umma mai lamba Cap A9 LFN na shekarar 2004 ya tabbatar.

A don haka lauyoyin suka roki kotun da ta umurci wadanda ake kara baki daya da su biya Naira miliyan 200 kowannensu saboda tauye hakkin ‘yan uwansu da suka kashe.

Haka kuma sun nemi kotun ta bayar da umurni ga wadanda suke kara da su rubuta takardar bayar da hakuri tare da bugawa a cikin jaridun kasarnan guda biyu da ke yawo a arewacin Nijeriya.

Sai dai wadanda ake kara, a cikin martanin su na farko mai kwanan watan 8 ga Nuwamba, 2022 wanda suka gabatar duk a wannan kwanan wata sun nemi da kotun ta bayar da umarnin soke kararrakin guda ukun.

Bayan hakan kuma, sun kuma gabatar da takardar shaidar adawa da wannan kararrakin.

Sai dai mai shari’a Buhari ta amince da kara da shaidun da lauyoyin masu kara suka gabatar, inda kuma ta yanke hukunci kan hakan.

 


No comments