Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Jami'o'in Amurka na fuskantar gagarumar zanga-zangar goyon bayan Falasɗinawa

  Daga Zailani Mustapha  An kama gomman masu zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa a jami’o’in Amurka, a yayin da daliban ke ci gaba da zafaf...

 


Daga Zailani Mustapha 

An kama gomman masu zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa a jami’o’in Amurka, a yayin da daliban ke ci gaba da zafafa zanga-zangar a jami’o’in. 

Dauki-ba-dadi mafi muni da aka yi shi ne na Jami'ar Texas a Austin, inda ‘yan sanda a kan dawaki suka hana masu zanga-zangar kafa sansani, sai kuma wadda aka yi a California. 

Zanga-zangar ta samo asali ne sakamakon kisan kiyashin da Isra’ila ke ci gaba da yi raunanan al’ummar Falasdinu. Inda dalibai a jami’o’in, suka soma gudanar da zanga-zangar nuna goyon baya ga al’ummar ta Falasdinu tare da kiran Amurka da ta tursasawa Isra’ila domin ta dakatar da kisan Falasdinu tare janye taimakonta ga Isra’ila. 

Wasu daga cikin jami’an gwamnati na kira da a dauki tsattsauran mataki a kan masu zanga-zangar, inda suke cewa masu akidar kyamar Yahudawa ne. 

‘Yan sanda a kan dawaki cikin damara, sun afka ma masu zanga-zangar a Jami’ar Texas inda suka kama gommansu. 

Wasu daga cikin jami'an gwamnatin Amurka na danganata zanga-zangar da masu tsattsauran ra’ayi da suka ce sun yi kutse ne cikin jami’o’in kasar da ake ta samun wannan ra'ayi na goyon baya ga Falasdinawa dangane da yakin da Isra’ila ke yi a Gaza. 

Zargin da masharhanta suka ce wata guguwar sauyi ce kawai ke aukuwa a Amurkan. Gwamnan jihar ta Texas Greg Abbott, wanda ya ce masu zanga-zangar sun fi dacewa da gidan yari, ya bayar da umarni ga rundunar tsaron kasar ta National Guard da ta kai dauki harabar jami’ar da ke Austin. 

Gwamnan ya ce ya kamata a kori daliban da suka shiga zanga-zangar da ya ce ta nuna kyamar Yahudawa ce. A Los Angeles ma ‘yan sanda sun afka ma dalibai masu zanga-zangar tare da kokarin cire wasu tantuna da masu zanga-zangar suka sanya. 

A yayin ziyarar da ya kai Jamia’r Columbia a New York shugaban majalisar wakilan Amurka Mike Johnson ya ce dole ne a kawo karshen zanga-zangar. Sai dai ya gamu da ihu daga daliban yayin da yake korafi da cewa an bar masu tsattsauran ra’ayi da ‘yan ta-kife su muzguna wa dalibai Yahudawa a zanga-zangar, in ji shi. 

Ya ce, “a yau na zo nan domin na sheda wa dukkanin wadanda ke kumaji da neman shafe kasar Isra’ila daga taswira da kai hari kan dalibanmu Yahudawa da ba su ji ba ba su gani ba, cewa ba daya daga cikinsu, Isra’ila ko wadannan dalibai Yahudawa da ke wannan jami’a da za su kasance su kadai.'' 

Grace Dai, wadda daliba ce a Jami’ar ta nuna bacin ranta a kan ziyarar shugaban majalisar wakilna Amurkar. Ta ce, ''ba ma tsammaninsa ko kadan. Ina ganin ya zo nan ne ya tayar da hankali. A gaskiya, ya haddasa bala’i a ko’ina. Ina ganin abin da ya sa muka yi masa ihu ke nan. 

Zanga-zangar nuna goyon baya ga Falasdinawa a jami’o’in Amurkar na ta karuwa tun bayan da aka kama sama da mutum dari daya da ke zanga-zangar a makon da ya gabata a Jami’ar Columbia. 

A martani ga masu kira da Shugaba Joe Biden ya dauki tsattsauran mataki a kan masu zanga-zangar kakakin shugaban, ya ce, Mista Biden ya yarda da ‘yancin muhawara, amma dole ne masu zanga-zangar su kasance suna yinta cikin lumana kuma ba tare da nuna kyamar Yahudawa ba.

No comments